Wani dan shekara 70 mai suna Sa’idu Isa, ya nemi kotun Shariar Musulunci dake Magajin Gari a jihar Kaduna da ta sanya a dawo masa da ragowar kudin sadakin da ya biya Naira 113,000 domin auren wata budurwa da aka ki aura masa bayan an karbi kudinsa.

Shi dai mutumin, ya shaidawa kotu cewar ya biya Naira 155,000 a matsayin sadakin wata yarinya da aka yi niyyar aura masa ta hannun wani mai suna Baba Haruna.

Malam Saidu Isa, ya shigar da kararwani Malam haruna,lokacin da ya samu labarin yarin da yake son ya aura tuni an aurar da ita ga wani.

“Na kashe kimanin Naira 155,000 domin auren wannan yarinya, amma sai suka dawo min da Naira 42,000, a sabida haka ina da ragowar cikon Naira 113,000, tunda sun riga sun aurar da yarinyar ga wani mutum daban” A cewarsa.

Wanda ake kara ya bayyanawa kotu cewar, ya karbi Naira 10,000 a matsayin kudin na gani ina so, sai kuma 60,000 a matsayin sadaki.

Yace ya dawo masa da 42,000 lakadan, sannan daga bisani ya aiko masa da ragowar 8,000 ta hanyar aika kudi daga wani asusu zuwa wani.

Ya bayyana cewar, Saidu Isa yayi niyyar auren ‘yarsa ne, ya kuma biya sadaki, amma daga bisani muka neme shi muka rasa, babu wai bayani da ya aiko mana har kusan shekara guda.

Wannan ce ta sanya muka yanke hukuncin aurar da ita ga wani daban tunda tana da masu son aurenta.

“Yarmu tana da masoya daga Abuja da suke neman aurenta, amma muka ki aura musu, sabida muna da alkawari da malam Saidu Isa, amma ya bata mana lokaci”

“A saboda haka, ba mu da wani zabi sai mu aurar da ita ga wanda yake son ta” A cewarsa.

Shaidu a lokacin malam Abduljalal da Malam Salamatu, sun bayyana cewar wani bangare na zancen Malam Saidu gaskiya ne, wani bangaren kuma ba haka abin yake ba.

Sun ce su ba su da wata masaniya kan cewar ya biya 155,000 a matsayin kudin sadakin auren wannan yarinya.

Alkalin kotun, Musa Sa’ad, ya bukaci duka bangarorin da su gabatar masa da shaidau da zasu tabbatar da maganar kowanne bangare.

Daga bisani aka dage sauraren karar zuwa 21 ga wannan watan, domin wanda ake kara da mai kara su gabatar da shaidu.

NAN

LEAVE A REPLY