Kasar Finlan ita ce kasa tafarko a duniya da mutananta suka fi farinciki a duniya, a cewar wani bincike wanda aka fitar da shi a ranar Laraba, inda binciken ya bayyana kasar Burundia matsayin kasa ta karshe a duniya wadda farincikin mutananta kadan ne, yayinda Najeriya ta samu matsayi na 91 a duniya.

Binciken kuma ya nuna cewar kasar Amurka da ta fi kowacce kasa arziki a zaman cewar mutanan kasar basa cikin farinciki sosai.

Sashin bincike da tabbatar da ayyukan na tafi daidai na majalisar dinkin duniya, shi ne ya fitar da rahoton wannan bincike akan kasashe 156, inda binciken yayi la’akari da karfin tattalin arzikin kasa da kiwon lafiya da walwalar ‘yan kasa da ‘yanci da kuma batun shekarun da mutane suka fiye mutuwa da kuma batun cin hanci a kasashen.

Kasar finlan ce dai ta samu cigaba sosai daga matsayi na biyar a shekarar 2017 zuwa matsayi na 1 a wannan shekarar, inda ta doke kasar Norway.

Kasa gome da suka fi zama cikin farinciki su ne, Finlan da Norway da Dinamark da Iceland da Suwizalan da Nezalan da kanada da Suwidin da kuma Austiraliya.

kaar Amurka ta zo a matsayi na 18 daga matsayin da ta ke kai da na 14 a shekarar 2017. Kasar Burtaniya ita ce ta zo a mataki na 19 yayin da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta zo a mataki na 20.

Rahoton mai shafi 170 yayi bayanin lafiya da ta damu kasashen da aka gudanar da binciken a cikinsa, da yawan kasashen suna fama da matsalar mahaukaciyar teba (Kiba) tunani ko mantuwa musamman a kasar Amurka.

 

NAN

LEAVE A REPLY