A kalla dalibai mata 80 ne a makarantar Sakindiren Gwamnati ta mata dake Mabera a jihar Sakkwato suka tsallake rijiya da baya, a sakamakon wata mummunar gobara da ta kama a dakunan kwanansu a ranar Lahadi.

Gobarar dai ta kone dakunan kwanan daliban kurmus, a gini mai suna Aish, babu rahoton da ya nuna asarar rai ko samun raunuka.

Tuni dai jami’an kwana kwana da sauran jami’an da suke tsaron makarantar suka ci nasarar kashe gobarar da aka ce ta tashi ne sanadiyar haduwar wayoyin lantarki.

Hukumar makarantar dai taki cewa komai dangane da batun, inda suka ce, ba su da hakkin yin magana da ‘yan jarida sai dai hukumar ilimi ta jihar.

Dukkan wani yunkuri na yin magana da ma’aikatar ilimi ta jihar da kuma jami’an hukumar kwana kwana ta jihar yaci tura, basa daukar waya, sannan basa duba sakon tes da aka aika musu.

 

NAN

LEAVE A REPLY