Marigayi Alhaji Wada Nas
Daga Ghali Sule Roggo
Assalamu Alaikum,
Amincin Allah ya tabbata a gare ka da sauran bayin Allah na gari da kuke tare. Ranka dade na dade ban rubuto maka takarda ba, ba don na manta da kai ba ne sai don abubuwan da ke faruwa a nijeria ya wuce hankalin mai hankali. kayi hakuri ban zo don in tada maka da hankali ba sai dai nazo na sanar da kai irin tabargazar da ake yi a kasar mu.
Ranka dade na san kana sane da lokacin da Allah ya kaddara zaka barmu ana shirin wani taron kasa da shugaban wancan lokaci watau Obasajo ya shirya don biyan bukatar kansa. Nasan ka fara shirya shiryan yadda jama’ar mu zasu je gurin taron da bukatun yankin namu. kwatsam sai Allah yayi kiran ka, Allah ya kara kyautata makwanci.
wannan karon ma shugabn wanna lokacin ya zo da irin waccan bukatar ta neman ya kau da hankalin mutane daga tabargazar da ake yi zuwa shirin ya sake dare kan kujerar mulki da taimakon kannen ka da abokan ka da suka juyawa arewacin kasar nan baya. An dai fara taro kuma jama’ar arewa sun tafi taron ba ashirye ba. kuma  kadan ne daga cikin su ke da sanin abin da ya akai su wajen taron.
Babban abin takaici shine wai yanzu an gane cewa kiristocin nijeria sun fi Musulumin yawa don Musulmi na 183 kiritoci na da 300 da wani abu. nasan zaka iya kintato abin da muke fuskanta a halin yanzu. bama wannan ne ya fi damuna ba sai kisan kare dangi da akewa yan arewacin Nigeria. ranka dade ba a kisan mutum daya yanzu sai dari a lokaci daya koma abin ya wuce haka. kwanan nan akayi irin wannan a mahaifar ka ta Katsina da Kebbi. Ban da wanda ke faruwa a Jos, Bauchi, Maiduguri, Adamawa, Yobe tunda gwamnatin nan ta hau jama’ar yanki basu sami kwanciyar hankali ba. Mutanen arewa suna ganin tashin hankalin da kaskanci iri-iri.
Nasan wannan zai bata maka rai kwarai ranka dade sai dai kayi hakuri, watau Mutanen arewa sun yi wata irin lalacewa ta rashin kishin jama’ar mu da yankin mu duk da wadannan abubuwan da ke nuna mana  rashin kaunar da akewa yankin da addinin mu, wasun mu ko ajikin su don su suna samun abin sawa a cikin miya. Ko kasan kanen ka da ke sakkwato kuma tsohon gwamna ya shiga rindunar durkake arewacin Nigeria tare da tsohon Malamin makarantar nan da Buhari ya daga hannun sa Allah ya aminta ya zama gwamna kano ya shiga cikin waccan kungiyar karya al’ummar arewa, bari na rage murna na gaya maka halin da Sunusi Lamido sanusi ya wayi kanshi da ya bayyana cewa wasu na kuruciyar bera da dukiyar yan nigeria, yana nan yana cikin wulakanci da tuzartawa duk da naga Malam Nasir el-rufai na taya shi jaje, amma duk arewa kowa ya kama bakishi yayi shiru. kuma kowa ya san gaskiya. Ina ka taba jin barawo ya shiga gida amma aka kasa cewa ga barawo sai barawo ya nuna mai gidan yace ai shima Dan fashi ne, sai mai gida kuma ya kuma cewa ga barawo. Kai wannan rai nin wayon yayi yawa kwarai.
Ranka dade baka da magaji yanzu a arewa, duk tsofaffin nan sun zama yan kasuwar bukata, in dai zasu samu shike nan kowa ma ya mutu, wannan shine abin da muke ciki. kasan shugaban dan asalin yanki da ake samun man fetru ne, yana da kudin sayen mutanen namu.
In zaka iya tunawa tun lokacin da Umaru musa Yar’aduwa ya ware kudi don yashe kogin kwara da fadadashi, amma Jonathan na hawa ya dakatar da aiki yace zai mai da kudin zuwa yankin sa na Neger-Delta, kuma hakan ta tabbata babu wanda yace komai.
Duk da wadannan alamu da ke nuna dan yatsa ga duk mutumin arewa, amma zakayi mamaki yadda yan arewa ke goyon bayan wannan dakilewar da ake mana don su zasu sami abin sawa a aljihun su. Yau Bafarawa, Tanko Yakasai, Buba Marwa da Shekarau duk suna jin dadin halin da arewa ta wayi kanta aciki. Babban abin takaici ma shine matsayin da matsan mu suka wayi kansu aciki na rashin KISHI! rashin sanin mutunci kai, rashin ganin kimar alummar mu.
Ranka dade nasan kasan Babangida, Abdulsalam, Aliyu Shehu Shagari, Gen. Gawon, Aliyu Gusau, Jibril Aminu, Adamu ciroma, ummaru dikko, Gen Danjuma Dukkan tsofaffin gwamnonin arewa da tsofaffin Ministocin nan da ka sani. Sarakunan Gargajiyya Duk sun koma yan amshin Shata babu mai cewa komai akan arewacin nigeria nasan wannan kasha fada cewa mafiya yawan su karyar arewa suke yi. lokacin da kayi ikirarin cewar babangida shine ummul aba isin halin da arewa ke ciki don neman yardar makiya.
Bari na dan tsegun tamaka halin da ganaral Buhari ke ciki yanzu, ya aminta da wani kawance da kudu maso yammacin kasar nan don gani ko Allah zai sa adace wajen ceton al’ummar mu. Amma fa yana fama da muna fukai daga cikin gida kuma yan uwan sa ake amfani da su don gurgunta tafia. kamar yadda na fada a sama. zan baka cikakken bayani a wasika ta ta gaba in sha Allahu.
zan dakata a nan sai na dawo na gaya maka, yadda aka shirya tsaf aka kai hari akan yan makaranta a nan arewa kuma jahar da ke karkashin jami’an tsaro ba tare da an kama ko gano wadanda sukayi hakan ba.
Ranka dade Dole na shaida maka cewar akwai wasu kannen ka da ke kokari gwargwadon hali kamar Dr. Aliyu Aliyu U. Tilde yana kokarin nusar da al’umma, Vision FM 92.1 a abuja suma suna kokari, Dr Nda na Leadership Newspapers ma ya na nuna karamci da kaunar mahaifar shi.
Zan dawo nan gaba don karasa bayanna da nake son sanar da kai. Allah ya kara kyautata makwanci dan kishin al’umma da sadaukarwa.
Na barka lafia.

LEAVE A REPLY