Alhaji Mamman Dangwate

Daga littafin Kano cibiyar Kasuwanci ta afirka wanda Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo Allah yajiqansa ya wallafa

Shi Muhammadu Dangwate ɗan Mallam Ali ɗan Shekarau, bafullatani ne mutumin kasar Kura ta jihar Kano.

An haife shi a wani gari mai suna Gwate dake kasar Nijar, a sanda Mahaifansa suka je garin domin fatauci a shekarar 1903 abar tunawa, wadda turawa suka zo Kano.

Bayan haihuwarsa ne sai mahaifansa suka komo garinsu Kura da zama, a can ne kuma ya taso tare da samun ilimin addini. An ce babban malaminsa sunansa Malam Ami, makarantarsa na nan a unguwar Tukuba layin Alhaji Ibrahim Maikarofi.

Bayan da Allah ya yi wa mahaifiyarsa mai suna Hadiza rasuwa, sai kakarsa mai suna Rabi ta nemi ya dawo hannunta da zama, ita kuma ta kasance tana zaune a cikin birnin Kano ne. Hakan kuwa akayi, domin mahaifinsa ya aminta da haka, inda ya dawo unguwar Makafin Dala ta birnin Kano da zama, anan kuma ya sauke littafin Alkurani maigirma, a hannun malaminsa mai suna Mallam Abubakar.

Daga bisani kuma sai kakar sa ta bashi jarin kuɗi sulai biyar domin ya soma taɓa kasuwanci da su. An ce Alhaji Muhammadu Dangwate ya soma ne da siyar da yadiddika anan unguwar Kududdufawa, sannan ya koma cinikin kwanika a ‘Yanmota ta kasuwar kantin kwari inda yakan siyi kaya daga hannun kamfanonin turawa irinsu Johnholt, GBO, UAC da kamfanin PZ na kasar Faransa.

Sannu a hankali sai Alhaji Muhammadu Dangwate ya shiga harkar siyasa, inda ya shiga jamiyyar N.P.C har kuma ya tsaya takarar ɗan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Kura. An ce ya samu nasarar lashe wannan zaɓe, inda suka shafe shekaru uku suna wakilci mai amfani ga alummarsu, watau daga shekarar 1963-1966.

Waɗanda suka rayu dashi, sun bayyana shi a matsayin mutum nagartacce wanda ba ya kin talaka, mai hakuri, mai taimakon nakasa gami da son abokai kuma.

Sannan ance yayi mu’amala da manyan mutane ta fannin siyasa da sarauta na lokacinsa.

An ce babban abin koyi a rayuwarsa shine tashi tsaye domin neman na-kai, kyauta tare da taimakon al’umma.

Shi ne akace akwai wata rana sanda aka haifi marigayi shugaban kasa Janar Sani Abacha, kasancewar attajiri Alhaji Abacha amininsa ne, ya halarci wurin raɗin sunan amma a makare. To anan ne wani maroki mai suna Gizo ya bishi yana masa roko da kirari yana neman kyauta gagaruma bisa wannan baiwar haihuwa da Allah ya baiwa abokinsa. Aikuwa nan take Alhaji Dangwate ya ce da marokin kaje nabaka duk kayan da ke jikina da kuɗaɗen aljihu na. Wohoho.. Wannan abu ya isa makura.

A lokacin an ce fam ɗari ne a aljihunsa, gashi kuwa kusan fam ɗaya ake biyan sadakin budurwa a lokacin. Haka kuwa bayan an gama taro Alhaji Dangwate ya cikawa wannan maroki alkwarinsa.

A fannin taimakon na kasa kuwa, ance akwai wani lokaci da Alhaji Muhammadu ɗangwate ya tura ɗansa Alhaji Garba Dangwate garin Maiduguri fatauci.

A wannan dalili ne sai ya haɗu da Alhaji Bukar Bolori, wani ɗan kasuwa ne shahararre a Maiduguri har kuma ya nemi yasan daga ina Alhaji Garba Dangwate ya fito.

Da ya tashi sai ya ke sanar masa ai sunan mahaifinsa Alhaji Muhammadu Dangwate.. Nan take sai aka ga jikin Alhaji Bukar Bolori yayi sanyi.

Daga baya sai ya ke sanar masa da cewa ai Alhaji Muhammadu Dangwate ne silar arzikinsa. Domin shine ke ɗora masa tallar kwanuka yana zagawa ya siyar, daga bisani yace masa ya komo garinsu zai rinka aika masa da kaya yana siyarwa.. A Haka har ya buɗe shago nasa, ya kuma zamo sahun attajiran Maiduguri.

Irin waɗannan labarai suna da yawa dangane da marigayin.

Allah ya yi masa rasuwa a shekarar 1966, ya bar ‘ya’ya 15, acikinsu harda Alhaji Aliko Dangwate wanda yake a matsayin Attajiri na ɗaya a faɗin Afirka.

Da fatan Allah ya ji kansa ya kuma kyauta namu zuwan amin.

(Daga Sadiq Tukur Gwarzo a Taskar Hikayoyi)

LEAVE A REPLY