Fatuhu Mustapha,masanin tarihi da al'adu

Daga Fatuhu Mustapha

A tarihin Kasar Hausa dama tsakiyar Sudan, tun shekaru sama da dari biyar, Kano ita ce gari mafi shahara a fannonin kasuwanci da siyasa, kusan banda Katsina ba wata kasa da ke iya kafada da Kano.  Rikicin Katsina da Maradi kusan shekaru 200 da suka gabata, ya jefa Kasar Katsina da tattalin arzikinta cikin mummunan hali, wanda hakan ya baiwa Kano damar tashin gwabron zabi, kuma hakan ya dace da lokacin da turawa suka fara karfi a nahiyar tsakiyar Sudan.  Wannan ya sanya koda da tsari irin na zamani ya zo, Kano ta dara sauran takwarorinta na kasar Hausa wajen kima da shahara da kasuwanci, kai har ma da siyasa.  A wasu lokuta a baya, Kano ta zama gagara gasa, a fannin tattalin arziki da cigaban siyasa a tsakanin jihohin  kasarnan, a wannan lokacin yan kasuwar Kano, sun zama abin kwatance a kasashen duniya, burga a wurin yan kasuwa shine; kamfanoni nawa ka kafa a Kano, ba yawan filaye ko katon gida ba.  Kusan bana mantawa har kamen mabarata ake a kaisu kamfani suyi aiki.

Amma kash! Yau Kano ta zama matattarar iyashege da sharholiya, kyashi, hassada da bakin ciki sun mana katutu, kullum wallen junanmu muke gani, ba kowa acikin Kano sai Yan aiki hujja  a siyasance, maaikatan gwabnatin barayi, fitsararrun samari, malamai yan tayi garas! Yan kasuwa marasa zuciya da imani, maaurata marasa amana, da sarakuna marasa hangen nesa.  Banda cin mutunci da tona asirin juna ba abinda muka sa a gaba, kowa jira yake yaga gazawar  abokin adawrsa ya tona masa asiri.

A kullum ka duba social media ko ka saurari labarai, baka jin komai akan Kano sai mummunan labarai, ga wanda bai taba zuwa Kano ba, zato zai in ya shigo Kano ba a komai sai fadan daba, shaye shaye, da zagin mutane.  Kuma babban abin takaicin, yan Kano suke yada wadannan munanan kalamai ga jihar tasu, walau dai da sunan: adawar siyasa, ko banbancin raayin addini ko kuma saboda kiyayya kawai.

Da kanmu muke batawa kan mu suna, ban taba ganin basakkwace ya yi rubutu ya zagi sarkin Musulmi ba, ban taba ganin bazazzage ya yi rubutu ya zagi sarkin zazzau ba, ko mutimin Bauchi ya ci mutincin sarkin Bauchi ba, Amma ba komai bane kaga mutumin Kano ya rubuta shafuka goma koma fi yana zagin sarkin Kano.

Mutumin Kano ne saboda aqidar banbancin siyasa ya kirkiri labarin under age voting a zaben kananan hukumomi da ya gabata, ya manta da cewa, anan gaba bamu da ta cewa a zabe, ko kuria nawa muka kawo, zaayi mana alkalanci ne da maganar under age voting da muka rataye kanmu da ita.

Tabbas ana shaye shaye a kano, na kwayoyi da ganye, Amma na yi imanin in da zaa yi bincike na gaskiya, akwai jihohin da suma haka abin yake, me yasa na Kano yafi na kowacce jiha kamari?

Amma abin tambaya anan, shin bawani abin arziki da Kanawa suke yi?

A hakikanin gaskiya abubuwan arziki da ke faruwa a Kano sun fi na tsiyar yawa, ko a lokacin da muka kaure da batun auren yar Ganduje, a daidai wannan lokacin, Dangote ya bude Dangote business school a Kano, amma Kanawa bamu damu ba, muna can muna yada fasadi na auren yar gwabna, muna korafin me yasa gwabnoni suka zo.

A Kano an kafa kamfanin matsar mai da yafi kowanne girma a Nigeria, kuma shugaban kasa da kansa yazo har Kano ya bude shi, wa ya damu?! Tunda duk Kanawa yan kwaya ne. Mun manta Gerawa Oil shine kamfani mafi girma a bangaren tatsar mai a Nigeria.

Daga shigowar gwamnatin Buhari zuwa yau, kanawa sun kafa kamfanonin taki (fertilizer)  zuwa casar shinkafa sun kai Takwas Amma ba wanda ya damu ya bada wannan labarin, an fi so aji fadan Kwankwaso da Ganduje.

Mun manta in ka ci mutincin wani shugaba a Kano, kaci mutincin Kano ne da Kanawa. In ka ci mutincin Kwankwaso ko Ganduje ko sarkin Kano, ko shekarau, kowani babban malami a Kano, ba wani ka taba ba, Kano ka taba.

Shi yasa dai ake mana kirari da : Marmara ci kan ki da kan ki.  Duk masifar da ka ga Kano ta shiga, Kanawa ne suka saka ta aciki.  Allah ya kyauta!!

 

LEAVE A REPLY