Daga Abdulrashin Ahmad
Zan fara daga Qureish, Ghaleb, Lou’ayy, Ka’ab, Murra, Kilab,Qusai (Sarkin Makkah), Abdul Munaf shi ya haifi Hashem da Abd Sham. Hashem ya haifi Abdul Mutallib, shi kuma ya haifi Abbas, Hamza, Abu Talib da Mahaifin Manzo (SAW) Abdullahi.
Zanyi bayani bisa wadannan ziri’a musu albarka ta daukar wasu daga cikinsu in fadi ziri’un su;
Gidan Hashem;
1. Abdullahi ya haifi Annabi Muhammadu (SAW) shi kuma ya haifi Fatimah (RA)
2.Abu Talib ya haifi Ali (RA) shi kuma ya auri Fatima diyar Annabi inda suka haifi Hassan da Hussain.
 a)Hassan (RA) zuri’ar ce tayi mulkin Makkah harzuwa lokacin da Ibn Saud suka koresu daga Hejaz (1925) sunyi hijira zuwa Jordan inda yanzu suke mulkin kasar tun daga 1920s. Wasu daga zuri’ar sa suke mulkin Marocco a yanzu.
 b) Hussein shi yayi shahada tare da iyalin sa a karbala ta kasan Iraq a yanzu. Wasu daga zuri’ar sa sun kafa Daular Fatimid a Misra (Ko da yake ta gushe shekaru daruruwa da suka shude) da Safavid a Iran. Haka magoya bayan Shi’a suna bin sane da zuri’ar sa.
3. Abbas zuri’ar sa ne suka kafa Daular Abbasaid a Baghdad bayan rushe daular Ummayyad. Sunyi mulkin daular musulinci tsawaon lokaci mai yawa, kuma a zamanin su Ilimin kimiya da fasaha ya daukaka har wasu daga cigaban da aka samu yanzu ya samo asali ne daga bincikin da akai a lokacin su.
Gidan Abd Shams.
Abd Shams dan uwane ga Hashem kakan Annabi (SAW), kuma shi ya haifi Umayya wanda daga sunansa aka samu sunan wadanda suka kafa Daular Ummayyad. Ummayya ya hafi;
a) Abul ‘As shi kuma ya haifi Affan da Al Hakam. Affan shine mahaifin Usman Ibn Affan (RA) sahabin manzo kuma surikinsa, Khalifa na uku bayan wafatin Manzo. Wasu daga zuri’ar Al Hakim suyi sarauta karkashin Daular Umayyad.
b) Harb ya haifi Abu Safyan (Sarkin Makkah), shi kuma ya haifi Mu’awuya wanda ya kafa Daular Ummayyad a Damascus.Dan shi   Yazid shi ya aika rundunar da ta kashe Hussein da iyalin sa.
Ina so mu lura, duk wadannan da na zano, Dangi daya ne. Akwai Annabi daya a cikin su Annabi Muhammadu SAW, Sahabbai tara (9) sanannu Abbas, Hamza, Usaman, Ali, Jaffar, Hassan, Hussein, Abu Safyan, Mu’awuya. Banda Sarakuna da manyan malamai da har zuwa yau ake dan gan tasu da su. Allah yai musu rahama, ya kuma yafai kura kuran su, Amin.

LEAVE A REPLY