Bello Muhammad Sharada
Filin Eagle Square a cikin tsakiyar Abuja nan ne nan da awa 18  cikin nufin Allah an fitar da sabbin shugabannin PDP na kasa, fili ya dauki harama. Mutane ne makil ‘yan jam’iyya cikin walwala da annashuwa, ana kade-kade da raye-raye. Ana cin kwalam da makulashe.
Wannan taro yana da muhimmanci kwarai, kuma zakaran gwajin dafi ne. Idan aka yi nasarar kammala shi  cikin  dadi PDP ta dinke tsaf, abin da yake gabanta shi ne tsara yadda za a tunkari APC a yi mata wuju-wuju a 2019. In aka samu matsala saboda son zuciya da biyan bukatar kai, sai dai lahaula, PDP ta koma garari, bayan wanda Sanata Modu Sheriff ya jefa ta ciki, kotun koli ta tsamo ta.
Yau PDP zata zabo mutum guda cikin takwas masu nema. Ko dai a zabi Olubenga Daniel, ko Tunde Adeniran ko Uche Secondus ko Jimi Agbaje ko Rashid Ladoja ko Taoheed Adedoja ko Akin Akintoye ko Raymond Dokpesi
Amma a hakikanin gaskiya wannan takarar a tsakanin mutum uku ce. Na daya Uche Secondus, wanda wasu gwamnoni masu ci suke son ya zama. Gwamnonin suna karkashin jagorancin na Rivers Nyesom Wike da na Ekiti Fayose.  Na biyu Tunde Adeniran, wanda dattijan jam’iyya da tsaffin gwamnoni suke mara wa baya.  Sannan sai Olubenga Daniel, wanda shi ma wasu tsaffin gwamnoni suke goyon baya.
Idan rarrashi da sulhu da ake kokarin yin don a bada mukamin ga Yarbawa ya kai ga cimma nasara, mukamin zai fada kan hannun Tunde Adeniran, shi ne dan takara da bai jingina da duk masu wata bukata ba ko wani gungu kuma  ba shi da masoka ta ciki gida ko ta waje. Idan sulhu bai yi ba, za a buga ne tsakanin Yarbawa da mutanen arewa suke goyon baya da ‘yan Neja Delta da suka hade kafafuwansu da Inyamurai guri guda.
Ba shakka PDP ya kamata ta maida hankali ta nutsu sosai domin samar da shugaba na kwarai da zai yi jagoranci managarci. Wannan zaben manuniya ce, kuma shi ne alkibla. Ita kanta Najeriya da jam’iyyar APC mai mulki tana bukatar PDP mai karfi, mai tsabta, ba gurguwa ba. Hakan shi zai taimaki dimokaradiyya, kuma shi ne zai dora tafarkin samar da zaratan shugabanni na jam’iyya da bada dama mai kyau ta samar da masu neman madafun iko da suka cancanta suka dace.
ABIN DA AKA KUNSO A ABUJA
Zuwa yanzu kowa ya koma gida daga taron fitar  da sabbin shugabanni  da zasu ja ragamar PDP zuwa shiga zaben 2019, har zuwa shekarar 2021. Wadanda basu koma gida ba zuwa hada wannan rahoto sune wasu ‘yan jam’iyya daga Garko ta Kano da aka yi garkuwa da su. Muna rokon  Allah ya kubutar da su daga wannan musiba da miyagu,Amin.
Tun daga ranar 12 ga Yuli 2017 wato ranar da kotun koli ta kori karar Sanata Ali Modu Sheriff, ta tabbatar da Sanata Ahmed Makarfi, manya da masu fada aji suka fara kulle-kulle. Duk wani kulli da ake yi, in ka bi shi tiryan-tiryan zai kai ka ga maganar babban zabe na 2019.
A tsakanin kusoshin jam’iyya, wato gwamnoni masu ci da tsaffin gwamnoni da tsaffin shugaban kasa da mataimakansu da sanatoci da  sojoji masu ritaya, zancen guda daya ne: yadda za a fuskanci 2019 a karbe ta daga hannun Muhammadu Buhari da APC kuma yaya kowa zai fidda kansa.
An yi zaben maslaha na ‘Unity List’ kowa ya haye kamar yadda gwamna Nyesom Wike na Rivers da Ayodele Fayose suka tsara. ‘Unity List’ shi ne jeren sunaye da aka yi tun kafin shiga zabe na yarjejeniyar ban gishiri na baka manda.
 Abubuwa uku wannan zaben ya nuna. Na daya har yanzu gwamnoni sune wuka da nama, gudanar da jam’iyya sai abin da suke so. Sanata Modu Sheriff ma wadannan gwamnonin biyu su suka kawo shi. Na biyu wanda duk bashi da zababben mukami komai gudunmawarsa a baya, tasirinsa kadan ne. Ina nufin irinsu Janar Babangida da Goodluck Jonathan da irinsu Farfesa Jerry Gana. Na uku kudi masu gidan rana suna canja kowane irin lissafi na siyasar Najeriya. Abin da ya sa na fadi haka Sanata Ahmed Makarfi, tsohon shugaban riko, a jawabin da ya yi a taron ‘convention’ ya ce a asusun jam’iyyar PDP na kasa babu ko naira miliyan biyu, ma’ana a wani gurin ake karbo kudade ake shirya taruka, wanda ya bada kudinsa kuwa shi ne da magana.
Abin tambaya anan shi ne menene ya sanya Ayodele Fayose gwamnan Ekiti, ya saryar da kujerar shugaban jam’iyya da dan jiharsa Farfesa Tunde Adeniran ya ke nema kuma kowa ya janye masa, ya gwammmace a bashi  matsayin ma’aji a kunshin shugabanci na kasa. Amsar ita ce Fayose zai bar gwamna a badi 2018, kuma yana son a bar masa dan takarar gwamna na dauki dora da ya zabo zai gaje shi, sannan idan PDP tazo  fitar da mataimakin shugaban kasa ya fito daga yankin Yarbawa, Fayose yana son wannan kujerar.
To shi kuma gwamnan Rivers Nyesom Wike mecece tasa bukatar? Amsa ita ce dayan uku ne. Zai shiga zabe a 2019 bai son a kawo shugaban jam’iyya  na kasa wanda ba dan hannunsa ba,  don kar a yi masa kafar ungulu, alhali ga irin hidimar kudi da yake yi wa jam’iyya. Ko kuma yana kan tsarin da Sanata Modu Sheriff ya  taba jefa zargi akansa, cewa sun kulla yarjejeniya su uku da shi da Atiku Abubakar da Uche Secondus zasu taimaki Atiku a lokacin shi Atikun yana APC. Watakila kuma yana share wa Sanata Ahmed Makarfi hanya ce ta takarar shugabancin kasa don wata bukatar ta dabam, kamar ta samun mai rufa baya.
Wannan zaben na ranar Asabat ya gudana cikin nasara da tsari, musamman in aka yi la’akari da cewa jam’iyyar APC mai mulki tun Oktoba 2014 har zuwa yau ta kasa shirya ‘Convention’ dinta.
A  inda  taron ya bar baya  da kura shi ne a wurin masu fada a ji na yankin Yarbawa ‘yan jam’iyyar PDP tunda an wofantar da bukatarsu, wacce aka yi yarjejeniya za a basu, sannan suna zargin an bi su da cin fuska. Magana ta gaskiya wannan zabe ya saka shakku a cikin zukatan Yarbawa, kowa ya san Bayerabe suna da dab’iar kwalo-kwalo amma zasu ga an yi musu kwan- gaba, kwan-baya anan. Mutum daya ne tilo ba shi da korafi a duk Yarbawa shi ne Ayodele Fayose dama kuma jiharsa ce kadai ta PDP. Sai sabon shugaban jam’iyya Uche Secondus ya yi aiki tukuru sannan za a iya shawo kan Yarbawa cikin tafiyar PDP. Suna da tasiri sosai, jaridu da gidajen rediyo da gidajen talabijin irinsu Channels TV, TVC, AIT da manyan masu tasiri a siyasar socialmedia, musamman Twitter da Facebook akasarinsu Yarbawa ne.
Wannan zaben ya nuna mana yadda za a yi zaben fidda gwani na masu takarar shugabancin kasa. Da gwamnoni masu ci da sauran zababbu a matakin  kasa da na jihohi zasu dunkule waje guda, tsaffin shugabanni, wato  tsaffin shugaban kasa da tsaffin gwamnoni da tsaffin ‘yan majalisa  da sauran masu fada a ji, suma zasu tare guri guda. Da akwai alamu ba za a yi la’akari da masu matsala da EFCC ba ko masu matsala a kotuna ko bukatar ‘yan jam’iyya na can kasa wajen fitar da mutum ba, maslahar ce za a yi amfani da ita amma wacce aka kudundune ta da kudi.
Ba shakka wannan zaben abin burgewa ne a siyasa, kuma ba tantama bai yi wa APC dadi ba, kuma ya nuna PDP balagaggiyar jam’iyya ce. Amma ko shakka babu karbar mulki a hannun APC  sai an yi da gaske, kuma sai an yi toshe-toshe, an kawar da son zuciya. A lokacin da APC ta ke son karbar mulki a hannun PDP da yawa irinsu Bola Tinubu da Kola Saraki da Atiku Abubakar sun  yi shahada sun jingine son zuciyarsu, in ba a samu haka ba a PDP aka kwatanta abin da aka yi a ‘convention’ akwai matsala kuma ita ce gaskiya.

LEAVE A REPLY