Daga Hassan Y.A. Malik

Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Rabiu Musa Kwankwaso ya sha alwashin yi wa abokin hamayyar shi, gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje ritaya daga siyasa a zaben 2019.

A wani sakon murya da ya aika gidan rediyon Express ta jahar Kano a jiya Laraba, Kwankwaso ya bayyana cewa babu abunda zai sauya masa wannan kudiri na shi.

Kwankwaso ya ce irin cin amanar da Ganduje ya nuna masa shi ne dalilin da zai sa shi ya dawo siyasar Kano ya kuma tumbuke shi daga kujerar shi.

Haka kuma sanatan ya sha alwashin yin waje da duk wasu ‘yan siyasar da ke da alaka da Ganduje, ko da kuwa a Abuja su ke.

LEAVE A REPLY