Alhaji Bola Ahmed Tinudu, Jagoran jam’iyyar AC na kasa baki daya, a ranar laraba yayi bayani dangane da batun wanda APC zata tsayar takara a zaben 2019.  Yace, jam’iyyar zata bi ka’idar Demokaradiyya wajen zaben mutumin da zai yi mata takarar Shugaban kasa.

Mista Tinubu yana bayyana hakan ne, a lokacin da yake zantawa da manema labarai, bayan wata ganawar sirri da yayi da wata kungiyar masu akidar yarabawa zalla ta Afenifere, ganawar dai an yi ta ne a gidan jagoran kungiyar ta Yarabawa zalla, Reuben Fasoranti dake birnin AKure na jihar Ondo.

“Babu wata Gwamnati da zata tabbatar da kanta a bisa mulki, Buhari mutum ne da yake son bin tsari da ka’idar da aka shimfida domin cimma kowanne irin kuduri” Inji Tinubbu.

“Buharin da na sani, ya yarda da bin doka da ka’ida. Dan haka ne, muke masa fatan, bin waccan tsari da muka sanshi na yin komai bisa doka, Gwamna Akeredolu ba Gwamna bane a lokacin da aka yi wancan tsari da ya samar da Buhari a matsayin dan takara, shima daliget ne na wancan tsarin”.

Ya kara da cewar, Shugabancin jam’iyyar APC bai sahalewa Buhari tsayawa takarar Shugaban kasa babu hamayya ba, a zaben Shugaban kasa da yake tafe nan gaba a 2019.

Tinubu yana wannan kalamai ne, a daidai lokacin da ake yada wata jita jitar cewar, Jam’iyyar APC ta sahalewa Buhari yin takarar babu hamayya a zaben 2019, wadda ake cewar Gwamnonin jam’iyyar sune suka ce sun sahalewa Buhari.

Tinubu wanda ya halarci wannan taro na kungiyar Yarabawa zalla tare da Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akredolu da mataimakinsa Agboola Ajayi, da mai rikon mukamin shugaban jam’iyyar APC na riko a jihar Ade Ademehin, yake bayyana cewar Shugaba Buhari mutum ne da ya yadda da bin tsari da ka’idojin da demokaradiyya ta shimfida.

Ya cigaba da cewar “mun bi dukkan tanade tanaden dokar tsarin mulkin jam’iyyaar APC kafin zabar Buhari a matsayin dan takara, dan haka ra’ayin wani mutum guda ko wasu, ba abin karba bane kan wannan batu.

Amma idan shugabannin jam’iyya da kwamitin amintattu da mu dukkanmu, muka zauna muka yi ittifakin cewar shi ne dan takararmu babu hamayya, to babu damuwa a ciki, zamu yi shi kuma mu bashi dukkan goyon baya, amma ba zikau wasu su ce sun sahale masa ba.

Za kuma mu tabbatar ba mu yi wasu abubuwa da suka saba da tanade tanaden hukumar zabe ta kasa ba, wajen fitar da duk wani dan takarar da zamu fitar.

“Abin da kawai kuke ji, makauniyar soyayya ce da wasu ke yi ga ‘yan takara. Buhari ba zai iya hana duk wani mai sha’awa tsayawa takara ba, ba kuma za’a yi hakan a jam’iyyar APC ba, zamu tabbatar ba’a danne hakkin kowane dan jam’iyya ba:.

 

 

LEAVE A REPLY