Shugaban jam'iyyar APC mai barin gado, John Oyegun

Daga Hassan Y.A. Malik

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, John Odigie Oyegun, ya bayyana cewa zuwa yanzu dai jam’iyyar ta warware matsalolin da ke nema keta ta gida-gida, kuma tuni ta dinke barakar da ke nema faruwa a jam’iyyar tare da amincewa su yi aiki tare.

Oyegun ya bayyana hakan ne a ofishin jam’iyyar ta kasa da ke Abuja a jiya Laraba bayan ya yi wata ganawa da gwamnonin jam’iyyar 5 da suka hada da: Abdulaziz Yari na Zamfara, Simon Lalong na Filato, Rochas Okorocha na Imo, Abdullahi Umar Ganduje na Kano da kuma Ibikunle Amosun na Ogun.

Kafin zaman gwamnonin da Oyegun sai da suka zauna da Shugaba muhammadu Buhari don su bayyana goyon bayansu ga kin amincewa da tsawaita shugabancin jam’iyyar da aka yi a kwqanakin baya.

“A yau, shugabancin jam’iyyar APC da kuma gwamnonin jam’iyyar sun zauna don kawo karshen matsalolin da ke nema su haifar da baraka a tsakaninmu. Mun kuma yi nasarar warware matsalar a wannan zama da muka yi don mu ci gaba da aiki kafada da kafada da juna don ci gaban jam’iyyarmu.”

“Tuni dai shugabancin jam’iyya ya kafa wani kwamiti don bayar da rahoton yadda abubuwa za su ci gaba daga inda aka tsaya.”

“Wannan kwamiti zai gabatar da rahotonsa a ranar Litinin a gaban shugabancin jam’iyyar a wani zama da shugabancin jam’iyyar ya shirya za a yi a ranar Litinin mai zuwa.”

“Jam’iyyar APC kanta a hade yake, kuma shugabancin jam’iyya na tare da Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnonin jam’iyyar,” Oyegun ya ce.

LEAVE A REPLY