Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko

Tsohon Gwamnan jihar Sakkwato Aliyu Magatakarda Wamakko, ya gargadi masu yunkuri kawo baraka tsakaninsa da mutumin da ya gaje shi a matsayin gwamnan sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, da cewar su sani hakarsu ba zata cimma ruwa ba.

Sanata Aliyu Wamakko wanda ke wakilatar Arewacin jihar Sakkwato a majalisar dattawa ta kasa, ya kara da cewar, da shi da Gwamna Tambuwal abu guda ne, dan haka babu wani abu da zai gitta tsakaninsu da zai sanya zullumi.

“Muna da manufa iri guda ni da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, dukkanmu burinmu shi ne cigaban jihar Sakkwato, dan haka mu duka abu guda daya ne, babu wani wanda zai ji kanmu, a matsayin tsohon gwamna da kuma mai ci”

Sanata Wamakko ya bayar da wannan sanarwa ne ta hannun mai magana da yawunsa Bashir Rabe Mani, wadda ya rabawa manema labarai, a gidan sanatan dake yankin Gawon nama a jihar Sakkwato.

Ina girmama Gwamna Tambuwal a matsayinsa na kanina, kamar yadda yake girmamani a ko da yaushe, shi (Tambuwal) mutumin kirki ne, babu wani sabani tsakaninmu, kuma ba za’a samu ba.

LEAVE A REPLY