Hukumar zabe ta kasa INEC, reshen jihar Oyo tace, akwai kimanin katin zabe 657,267 wanda aka buga shi na ‘yan jihar amma babu wanda yazo ya karba.

Babban sakatare a hukumar, Surajudeen Junaid ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yayi a birnin Badun na jihar ta Oyo.

Mista Junaid ya bukaci duk wadan da suka san suni katin kuma basu karba ba,da su gaggauta zuwa domin karbar katinsu.

Sannan ya bukaci duk wani matashi da ya kai shekarun yin zabe da ya je ya yanki katin zabe a mazabarsa.

Ya kara da cewar, ya kamata ‘yan Najeriya su sani cewar, ‘yancin su ne su yi katin zabe domin zabar Shugabannin da zasu shugabance su a matakai daban daban.

Sannan yayi kira ga ‘yan siyasa da su guji dukkan wani yunkuri da zai tayar da hayaniya a lokacin zabubbuka.

hukumar zabe ta shirya tsaf domin wayar da kan mutane kan batun zaben da ke tafe.

LEAVE A REPLY