A safiyar yau ne aka kaiwa kanin Abdullahi Abbas Sunusi Kwamishinan ma’aikatar Ayyuka na musamman, mai suna Walid Abbas Sunusi farmaki a unguwar Chiranchi dake yankin karamar hukumar Gwale. Shi dai Walid Abbas Sunusi ance dan Kwankwasiyya ne da yake adawa da yayansa Abdullahi Abbas na Gandujiyya.

A kwanakin baya an jiyo Abdullahi Abbas Sunusi nakiran magoya bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da su yiwa Kwankwaso da magoya bayansa jifan Shedan a ziyarar da ake sa ran kwankwason zai kawo Kano nan gaba a karshen watan nan.

Al’umma da dama na fargabar yanayin da siyasar Kano zata tsunduma a ciki a tsakanin bangaren magoya bayan tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da kuma na magoya bayan Gwamna Ganduje.

Bayanai sun ce an garzaya da wadan da suka ji raunuka zuwa abisiti domin basu magani. Wani da abin ya faru a kan idonsa da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa wakilinmu cewar “Naga mutane da makamai tsirara akan titi suna yawo suna neman ‘yan kwankwasiyya”

LEAVE A REPLY