Shugaban Jam'iyyar PDP na kasa Uche Secondus

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus, ya tofa albarkacin bakinsa kan kalaman da aka jingina su ga tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, inda ya bukaci al’ummar Najeriya da kada su kuskura su zabi SShugaba Buhari a 2019.

A cewar Shugaban PDP na kasa, wannan maganganu na IBB sun tabbatar da abinda jam’iyyar PDP take fada kan Shugaba Buhari. A cewarsa wannan magana ta IBB ita ce masayar jam’iyyar PDP.

A ranar lahadi ne dai, tsohon Shugaban kasa Ibrahim Badamasi babangida ya fitar da wata sanarwa da yayi kira ga ‘yan Najeriya da kada su zabi Buhari a 2019. Inda ya shawarci Buhari da kada ya nemi tazarce.

A cewar Mista Secondus, “Wannan shi ne abinda jam’iyyar PDP ta sha nanatawa game da Shugaba Buhari, inda yace jam’iyya mai mulki ta gaza biyan bukatun ‘yan Najeriya”

Shugaban PDP din yace, Jam’iyyar APC mai mulki ta gaza ta kowanne fanni, domin babu abinda ta yiwa ‘yan Najeriya, a cewarsa, PDP ce kadai jam’iyyar da ta dace da ‘yan Najeriya, kasancewar tana da gogewa da kuma fahimtar yadda najeriya take.

Ya cigaba da cewar “Jam’iyyar PDP na yin aiki tukuru wajen ganin ta sake darewa kan karagar Mulki a 2019, domin ceto Najeriya daga halin durkushewar da take neman yi a hannun jam’iyyar APC”

Mista Secondus yana yin wannan jawabi ne a lokacin da dubun dubatar magoya bayan jam’iyyar PDP suka tarbeshi a birnin Asaba na jihar Delta a ranar Lahadi.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su mallaki katin zabe, wanda shi ne makamin da zasu kifar da wannan gwamnatin da shi a cewarsa.

LEAVE A REPLY