A wani yanayi na shirye-shiryen tunkarar zaben 2019, jam’iyyun siyasa guda 22 sun kulla kawance da nufin hada karfi da karfe wajen ceto kasar nan daga halin da ta ke cike na abinda suka kira rashin iya jagorancin jam’iyya mai mulki, inda tuni wannan gamayya ta kira taron wakilan jam’iyyun jiya Juma’a, a birnin tarayya Abuja, inda suka tattauna yadda za su tunkari zabe mai zuwa da kuma yadda za su fuskanci jam’iyya mai mulki don ganin an samu sauyi a Nijeriya.

Wannan kawance na jam’iyyu da suka kira kansu da  Committee of Concerned Political Parties (CCPP), (Kwamitin Jam’iyyun Siyasa Masu Kyakkyawan Fata Da Manufa Ga Kasa) sun tabbatar da cewa zamansu na jiya ya haifar da wasu kwamitoci har guda 6, kuma kowane kwamiti zai fitar da rahoto game da aikin da aka bashi. Wadannan rahotanni dai sune za su zama manufofin gamayyar jam’iyyun na bai daya.

A wata sanarwar bayan taro da gamayyar jam’iyyun suka fitar, wacce Dakta Anwubuya Abraham wanda shi ne shugaban gamayyar jam’iyyun ya karanta ta ce: An kafa wani kwamiti da zai yi nazari tare da fitar da kudurorin jam’iyyun na bai daya.

Shugaban ya bayyana cewa: Babban muradin gamayyar jam’iyyun ta CCPP shi ne na zakulo hanyoyin da za a fitar da Nijeriya daga cikin kangin matsalolin da suka addabeta wadanda suka hada da rashin zaman lafiya da ke neman farraka kasar.

Daga cikin jam’iyyun da suka samu wakilci a zaman na jiya sun hada da: Freedom and Justice Party (FJP), Sustainable National Party (SNP), New Nigeria People Party (NNPP), Social Democratic Party (SDP), Allied Congress Party of Nigeria (ACPN), Unity Party of Nigeria (UPN) da kuma National People’s Congress Party (NPC).

Kwamitocin da zaman CCPP na jiya haifar sun hada da: Kwamitin sauya fasalin kasa da tuntuba tsakanin gwamnatoci, Kwamitin harkokin tsaro da sulhu, Kwamitin kasafi da tsare-tsare da, Kwamitin tuntuba, Kwamitin bincike da alkinta bayanai.

LEAVE A REPLY