Shugaban jam'iyyar APC na kasa John Odigie Oyegun

Jam’iyyar APC mai mulki, ta bayyana yunkurin jam’iyyar PDP na cinye jihar Legas a zaben 2019 da cewar wani abin dariya ne.

Mataimakin jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar reshen jihar Legas Abiodun Salami ne ya bayyana hakan a ranar laraba, yace ko kadan wannan mafarki na PDP ba zai tabbata ba.

Ya bayyana cewar, jam’iyyar PDP babu ita babu kayanta a jihar Legas, zancen zasu cinye jihar Legas a zabe mai zuwa, wannan mafarki ne kawai.

Mista Salami yana maida martani ne ga maganar da Kakakin jam’iyyar PDP a Legas din yayi inda yace PDP na yin duk kokarin da zata iya wajen ganin ta cinye jihar Leags a zaben 2019 dake tafe.

Taofik Gani, shi ne kakakin jam’iyyar PDP a jihar Legas, ya bayyana a ranar Talata cewar, a zaben 2019 PDP zata yiwa jam’iyya mai mulki APC zigidir a jihar Legas.

YA bayyana cewar, mutanan jihar Legas sun gaji da mulkin kama-karya na APC a jihar Legas. Babu wani abun ku zo mu gani da APC take tabuka mana, dan haka mutane sun kagu su yi waje da APC.

“Zamu baiwa APC mamaki a 2019. Ku shaida zance na. Muna da dukkan wasu dabaru da zamu yi amfani da su domin kawar da APC daga jihar Legas”

“AMma ya zuwa yanzu, muna nan muna aiki ta karkashin kasa domin ganin PDP ta samu nasara a jihar Legas”

“Ambode ya bamu kunya, bai tsinana komai. Babu abinda muke gani sai farfaganda da ake yiwa ‘yan Legas da sunan canji, amma hakikanin canjin da ake bukata shi ne PDP ta cinye jihar Legas” Inji Mista Gani.

Amma kuma a nasa bangaren Salami yace ‘yan adawar ba su da komai tamkar kwale kwale ne da bai dauki komai bayake yawo akan ruwa, yace al’ummar jihar Legas sun gamsu da APC zasu kuma zabenta a dukkan zabubbuka.

NAN

LEAVE A REPLY