Hassan Y.A. Malik
Akalla gwamnonin jam’iyyar PDP guda shida aka hanga a gidajen saukar baki daban-daban na gwamnatin Gombe, inda tuni rahotanni suka gwada cewa gwamnonin za su yi wani taro ne da za a fara shi da misalin karfe 9:30 na daren yau Lahadi.
Daga cikin gwamnonin da suka fara sauka a jihar ta Gombe sun hada da: Gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, sai gwamna  Ben Ayade, Emmanuel Udom, Ifeanyi Okowa, Darius Ishaku, Victor Okeze Ekpaezu da kuma mataimakin gwamnan jihar Bayelsa.
 Sauran wadanda za su halarci taron na yau sun hada da kafatanin shugabannin jam’iyyar na jihohi 36 da Abuja da kuma sakatarorinsu.
Ko da yake dai ba a bayyanawa manema labarai dalilin taron na yau ba, amma hasashe na gwada cewa gwamna Dankwambo ne ya kira taron don ya nemi goyon bayan mahalarta taron su bashi hadin kai don ya yi wa jam’iyyar takarar shugaban kasa a shekarar 2019.
Shugaban jam’iyyar ta kasa, Uche Secondus ne zai jagoranci taron.

LEAVE A REPLY