Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar

Uwar jam’iyyarAPC ta kasa, a ranar Lahadi ta bayar da sanarwar kafa wani kwamiti wanda zai jagoranci shirya taron kasa na jam’iyyar, wanda Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar zai kasance shugaba.

A cewar, Shugaban mai lura da tsare tsare na jma’iyyar APC, Osita Izunaso, a wata sanarwa da ya bayar ta shafin yanar gizo na jam’iyyar, inda yace mambobin kwamitin sun kai mutum 68, ciki kuwa sun hada da Gwamnan Imo da na Borno da na Katsina da na Oyo da na Yobe da na Kaduna da na Filatu da na Adamawa da na Kogi da kuma Gwamnan Edo.

Daga cikin mambobin wannan kwamitin, ya kunshi tsofaffin Sanatoci da kuma masu ci, da kuma mabobin majalisar wakilai ta tarayya da jiga jigan jam’iyyar na kasa. Kwamitin dai yana da Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu a matsayin Sakatare, sai kumaSanata Ben Uwajumogu a matsayin mataimakin Shugaban kwamitin.

Jaridai DAILY NIGERIAN ta jiyo cewar, masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, sun amince da nadin Gwamna Badaru, bayan da aka kai ruwa rana kan wasu sunaye da aka bijiro da su domin basu mukamin.

Tunda fari dai zababbun Gwamnonin jam’iyyar ne suka amince da nada takwaransu Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar a matsayin wanda zai Shugabanci kwamitin.

NAN

LEAVE A REPLY