Injiniya Buba Galadima

A tattaunawar da yayi da sashen Hausa na BBC, Injiniya Buba Galadima yace gwamnatin tasu ta APC da suka yi uwa suka yi makarbiya domin ganin kafuwarta, bata tsinanawa al’ummar Nigeria komai ba ya zuwa yanzu.

Galidima yace, sam bai gamsu da salon yadda ake tafiyar da gwamnatin Muhammadu Buhari ba. Sannan ya soki batun tsaro da yaki da rashawa. Ya kalubalanci jami’an tsaro cewar “ba zasu iya tuka daga Damaturu zuwa Damasak su kadai ba” yace sam batun da ake na tsaro rufar kura ne da fatar akuya.

Sannan Galadima, yace an yi watsi da wanda duk suka yi tallar Buhari tun farkon fitowarsa takara. Ya kara da cewa, “babu ko mutum daya da aka baiwa mukami a cikin mutanen da suka tallata Buhari tun farkon shigarsa al’amuran siyasa.

Da aka tambaye shi dangane da zaben 2019, Buba Galadima yace, ba zai ayyana wani mutum a matsayin wanda zai marawa baya a yanzu ba, a cewarsa akwai lokaci nan gaba da zai yi hakan. Da aka tambaye shi ko zai marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya, yace indai ba a neme shi ba ba zai kai kansa ba. Ya kara da cewar, yafi karfin yaje a samu wani dan siyasa yace zai taimaka masa ko waye.

Me zaku ce kan wadannan bayanai na Buba Galadima da yayi a BBC?

LEAVE A REPLY