Tsohon Gwamnan jihar Katssina Ibrahim Shema

Tsohon Gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema, ya ce, ya tafi ya barwa sabuwar Gwamnatin jihar Katsina zunzurutun kudi,Naira biliyan 14 a asusun gwamnatin jihar a 29 ga watan Mayun 2015.

A wata sanarwa da mai taimakawa tsohon Gwamna kan mu’amala da ‘yan jarida, Oluwabusola Olawale, tsohon Gwamnan ya musanta zargin da Gwamnatin Katssina mai ci karkashin Aminu Bello Masari inda ta yi ikirarin samun Naira biliyan 4 kacal a asusun gwamnatin jihar.

Sanarwar ta cigaba da cewar “Idan har Gwamna Aminu Bello Masari yana da gaskiya a wannan ikirarin da yayi, to  ya wallafa, dukkan bayanin asusun Gwamnatin jihar Katsina a jaridun kasarnan, domin tabbatar da abinda yake fadi gaskiya ne ko akasinta”

Haka kuma, Tsohon Gwamnan ya karyata Gwamnatin Masari ta yanzu da take ikirarin cewar tsohon Gwamnan ya tafi ya bar mata tarin bashi, “Mun kalubalanci Gwamnatin Masari da ta wallafa duk wata wasika da ta ke dauke da bayanin karbar bashi da Shema yayi indai yana da gaskiya”

“Babu kanshin gaskiya akan ikirarin da Gwamna Aminu Bello Masari yayi na cewar, shi ne ya kammala dukkan wasu ayyuka da Gwamnatin Shema ta bari, mun biya dukkan kwangilolin da muka bayar kafin mu bar Gwamnati” In kuma ikirarin Gwamna Masari gaskiya ne, ya bayyana a jaridu domin tabbatar da gaskiyarsa da kuma karyata abinda muka fada.

LEAVE A REPLY