Goodluck Ebele Jonathan

Daga Abba Wada Gwale

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba ta taɓuka komai ba, kuma ta kasa cikawa ’yan Najeriya alƙawarurrukan da ta yi musu lokacin da take yaƙin neman zaɓe.

Jonathan ya ce maimakon gwamnatin APC ta yi ƙokarin sauƙaƙawa ’yan Najeriya ƙuncin da suke ciki, sai wahala da fatara aka sake saka ɗan Najeriya a ciki ta hanyar manufofi marasa fa’ida.

Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a ofishinsa dake birnin tarayya Abuja lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar tsohon ministan ilimin ƙasar nan kuma ɗan takarar shugabancin jam’iyyar PDP, Farfesa Tunde Adeniran.

Ya ci gaba da cewa gwamnatin APC wadda ta dinga sukar gwamnatinsa lokacin yana mulki babu wani abu da zata iya nunawa al’umar kasar nan wanda tayi musu cikin shekaru biyu data yi tana mulki.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Buhari ba zata iya tsayar da wutar lantarki ba a ƙasar nan ba, kuma hakan ya sa masana’antu suna rufewa saboda rashin wuta.

Da yake magana akan shugabancin jam’iyyar kuwa, Jonathan yace jam’iyyar tasu ta PDP a wannan lokaci tana bukatar shugaba wanda zai jajirce don ganin sun karɓi mulki a hannun APC.

“Litar man fetur yanzu naira 145 ce, sannan babu wutar lantarki. Saboda haka muna buƙatar shugaba nagari a jam’iyyar mu wanda zai yi ƙoƙarin ganin mun samu ɗan takara nagari domin mu dawo mulki mu ci gaba da kawo ayyukan alheri,” inji Jonathan.

Sannan ya ce nan gaba kaɗan zai tsunduma cikin harkokin siyasa domin ganin jam’iyyar ta fitar da ɗan takara wanda zai karɓi mulki a zaɓe mai zuwa.

Ya ce PDP tana buƙatar shugaban jam’iyya kamar Farfesa Adeniran wanda ba kawai taimakawa zaiyi ba wajen samun nasara a zabe, zai ci gaba da bawa shugaban ƙasa shawara don kawo ayyukan cigaba.

Ya kuma ja hankalin ’yan takarar cewa duk wanda ya samu nasarar lashe zaben shugabancin jam’iyyar dole ya tafi da duk ’yan jam’iyya domin ganin an cimma gashi.

Farfesa Adeniran, wanda kuma tsohon jakadan Najeriya ne a ƙasar Jamus ya ce tuni jam’iyya mai mulki ta APC ta fara shirye-shiryen bawa PDP mulki a shekara ta 2019, domin babu abinda su ka yiwa ’yan Najeriya.

LEAVE A REPLY