Sanata Ali Ndume

A Najeriya, a karshen makon da ya gabata ne wata kotua birnin tarayya Abuja ta baiwa majalisar dattawa umarnin mayar da Sanata Ali Ndume zauren majalisar bayan da ya shafe takwas a matsayin datacce dan majalisa.

Bayan haka kuma, kotun ta bayar da umarnin a biya Sanata Ndume dukkan haƙƙoƙinsa na watanni takwas din da yayi baya majalisar. Shin ko wannan zai zamarwa Sanatan izna ga barin yiwa dokokin majalisar karan-tsaye? Ga abinda Sanatan ke cewa:

“Alhamdulillah, kotu tace majalisar dattawa ba tada hurumi ta dakatar da dan majalisa sama da kwana 14, idan har laifinsa yayi tsanani, misali ace yayi fada da wani, duk da ni abinda ya faru ba fada nayi da wani ba”

Na jawo hankalin majalisa ne akan zargin da ake yi mata, na bata suna, kuma aka bincika wanke duk wanda ake zargi ni kumamai makon a yaba min, sai aka hukunta ni aka dakatar da ni daga dukkan harkokin majalisar”

“Yankin da nake wakilata a majalisar sun yi babbar asara ta rashina a tsawon wannan watanni takwas din da nayi bana halartar zaman majalisar, domin akwai hanyar da take ci mana tuwo a kwarya wato hanyar Gombe zuwa Biu, da yake bana nanbabu wanda ya bi sawun wannan aiki”

“Idan har nayi kuskure zan iya bayarda hakuri ga majalisa, tunda ni dan adam ne,zan iya yin kuskure kuma zan iya yin daidai”

 

 

LEAVE A REPLY