Atiku Abubakar
Atiku Abubakar

Wani jigo a jam’iyyar APC, Cif Jackson Lekan Ojo wanda shi ne shugaban wata kungiya ta matsan kabilar Yarbawa ta Yoruba Youth Alliance (YYA), ya bayyana cewa a shirye ya ke da ya yi wa tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar yakin neman zabe a zaben 2019.

Cif Ojo ya bayyana Atiku a matsayin mutum daya tilo da zai iya kayar da Buhari a zaben 2019 cikin sauki.

Ya ci gaba da cewa wadanda ke zargin Atiku da yin ba daidai ba saboda ya fice daga jam’iyyar APC ba su fahimci siyasar Nijeriya bane.

“Mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar shi ne ke da karfi na siya da zai iya taimakawa PDP ta kawar da APC daga mulki a shekarar zabe ta 2019.”

Jaridar Daily Trust ta rawaito Cif Ojo na cewa, “Zai yi wa PDP matukar kyau in Atiku ya samu takarar karawa da Buhari, domin jam’iyyar ba ta da gogaggen dan siyasa da ya kai Atikun”

A cewar Cif Ojo, Atiku na da basirar gina dan adam ta hanyar fito da hanyoyin sana’o’i da kasuwanci daban-daban, kuma wannan zai sanya Atiku Abubakar ya soyi a rayukan ‘yan Nijeriya.

A kasashen Afirka da dama, mun ga yadda jam’iyyun adawa suka kayar da jam’iyya mai mulki. An yi a lokacin Goodluck Jonathan saboda yanzu ‘yan Nijeriya sun waye yanzu, dan takara suke zaba ba jam’iyyara siyasa ba.

Naij.com a kwanakin baya ta rawaito cewa jam’iyyar PDP ta hana Atiku da magoya bayansa su lika fastocinsu a yayin babban taron jam’iyyar da aka yi Abuja. Haka kuma jam’iyyar PDP ta hana sauran masu neman kujera lamba daya a Nijeriya da suka hada da Sule Lamido, Ibrahim Shekarau da Ayo Fayose da su ma kar su daga fastocinsu a wajen taron.

LEAVE A REPLY