Mai neman kujerar Shugabancin jam'iyyar APC ta kasa Adams Oshiomhole

Tsohon Gwamnan jihar Edo, Kwamared Aliyu Adams Oshiomhole ya bayyana cewar zai kaddamar da takararsa ta neman kujerar Shugabancin jam’iyyar APC ta kasa a ranar Alhamis dinnan.

Oshiomhole ya shaidawa ‘yan jarida a birnin Benin na jihar Edo cewar, Shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki da Kakakin majalisar dokoki ta kasa Yakubu Dogara suna mara baya ga takararsa ta zama Shugaban jam’iyyar APC na gaba.

Haka kuma, ya bayyana cewar, Shugaban kungiyar Gwamnonin jam’iyyar APC kuma Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha shi ne zai jagoranci Gwamnonin jam’iyyar wajen bikin kaddamar da takarar Oshiomhole da za’a yi a otal din Hilton dake Abuja.

Daman dai, tuni Adams Oshiomhole ya samu sahalewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen neman Shugabanci jam’iyyar na kasa.

Oshiomhole ya bayyana cewar ya shiga neman kujerar Shugabancin jam’iyyar na kasa ne domin shima ya bada tasa gudunmawar wajen ganin an gina jam’iyyar tare da shi.

LEAVE A REPLY