Abdullahi Abbas, Kwamishina a Ma'aitar Ayyuka na musamman a jihar Kano

Abdullahi Abbas Sunusi, shi ne kwamishinan ma’aikatar ayyuka na musammana jihar Kano. A wani faifan bidiyo da jaridar TheCable ta samu, an jiyo Abdullahi Abbas yana baiwa wasu matasa umarni da su yiwa tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso jifan Shaidan idan yazo Kano.

A cikin bidiyon an ji Abdullahi Abbas yana cewa “Ina godiya ga Gwamna Aganduje,kuma ina mai tabbatarwa da magoya bayan jam’iyyarmu cewar a yau, an busa wusur din siyasa a jihar Kano,musamman ga ‘yan adawarmu na cikin gida (Magoya bayan Kwankwaso) mun kafsa da su a lokacin hawan Sallah a kofar kudu sun kwashi kashinsu a hannu.

“A yanzu kuma wai jagoransu zai zo Kano, za kuma mu karbe shi a kwanar dangora ko Dakatsalle, kun san cewar ko a hajji abu na kashe shi ne, jifan Shedan, asabida haka, ku zama cikin shiri na sanarwa ta musamman da zaku ji akan wannan jifan da zaku yiwa Kwankwaso”

“Bama tsoron kowa, kuma duk wanda yace mana kule munce masa chass, a sabida haka dole mu hada karfi da karfe domin mu wargaza siyasar Kwankwaso kamar yadda kuka sani yana tsoronmu matuka”

Wannan shi ne abinda aka jiyo Abdullahi Abbas yana cewa a cikin bidiyon da aka nada. Sai dai babu bayanin a inda yayi wannan magana, domin ba’a bayyana wajen ba a cikin bidiyon.

LEAVE A REPLY