Sanata Shehu Sani

Sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Shehu Sani a ranar lahadi ya bayyana cewar jam’iyyarsu ta APC da Shugaban kasa Muhammadu Buhari suna da jan aiki a gabansu kafin su samu nasarar zaben 2019.

Sanata Shehu Sani, shi ne Shugaban kwamitin majalisar dattawa mai lura da bashi na cikin gida da na kasashen waje, ya bayyana hakan ne a birnin Badun da jihar Oyo lokacin wani taro.

Yace jam’iyya mai mulki ta auku cikin rikici ko ta ina kusan tun shekarar 2015, yace wadannan rigingimu da jam’iyyar take fama da su zasu iya kai keyar jam’iyyar kasa a zaben 2019 matukar ba a zauna an nemi mafita ba.

“Ina da yakinin cewar aikin da ke gaban Jagoran jam’iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zo a lokacin da ya dace, ina kuma fatan zai samu nasara a aikin nasa”

“Daga cikin matsalolin jam’iyyar da ya kamata a yi musu duba na tsanaki sun hada da takun saka da sabani dake tsakanin Gwamnoni da ‘yan majalisar dattawa na jihohinsu, sannan kuuma dinke barakar dake tsakanin ‘yan majalisar tarayya da jam’iyya a jihohinsu”

“Sannan akwai gagarumar wuta tanna ci bal bal tsakanin ‘yan majalisar dattawa da kuma ‘yan majalisar zartarwa ta Shugaban kasa” A cewar Sanata Shehu Sani.

Ya kara da cewar dole ne jam’iyyar APC ta dinke dukkan wannan barakar sannan ta iya tunkarar zaben 2019 sannan ayi tunanin samun nasara.

Sanatan ya cigaba da cewar Gwamnatin APC a Najeriya ba za’a ce bata samu nasara a wasu bangarori ba, idan muka kalli bangaren tsaro da batun yaki da ta’addanci an dan samu nasara ta wannan bangaren.

“Ta bangaren tattalin arrziki kuwa, an samu raguwar ayyukan cin hanci da rashawa, amma kuma batun kashe kashe da ake yi a wasu bangarori na kasar anan matsala ce babba idan ba’a tashi tsaye a kanta ba”

A cewarsa, wadannan kashe kashe da ake yi abin Allah wadai ne, dole ne kuma a tashi domin kawo karshen abin.

Sanatan ya bayyana yankin kudu maso yamma da cewar shi ne kashin bayan jam’iyyar APC a Najeriya, idan bangaren kudu maso yamma na jam’iyyar APC ya samu matsala to zata iya shafar nasarar jam’iyyar a dukkan matakai.

Haka kuma, Sanatan ya soki batun kirkiro da ‘yan sandan jihohi da wasu Gwamnoni suke son lallai sai anyi.

“Rikicin da muke fama da shi a jihar Kaduna batu ne na cikin gida a APC, rikici ya kai wannan jallin ne sabida uwar jam’iyya ta jihar ta gaza yin abinda ya dace ta yi, har abin ya kai ga rusa Sakatariyar jam’iyyar da Gwamna yayi”

“Akwai abin mamaki,idan har za’a ce Gwamnan da ya hau mota ya rushe ginin sakatariyar jam’iyya kuma ace an bashi damar kafa ‘yan sandan jiha mallakarsa, me muke zaton zai faru da irin wannan Gwamna din?”

NAN

LEAVE A REPLY