Attahiru Bafarawa

Gamayyar kungiyar matasan jam’iyyar PDP reshen yankin Arewa maso yamma, bayan wani zaman gaggawa da suka gudanar a ranar Alhamis, sun bukaci tsohon Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa da ya daure ya tsaya takarar Shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben 2019.

Jagoran matasan yankin, ya shaidawa majiyar THISDAY, inda yace wasu daga cikin jiga jigan mutane daga Arewacin Najeriya,karkashin wata kungiya mai suna ‘Northern Coalation Force’ sun hadu a Birnin-Kebbi a jihar Kebbi domin tattauna makomar kasarnan.

A cewarsa, matasan sun tattauna akan makomarNajeriya, da kuma samun wani ingantaccen dan takarar Shugaban kasa wanda zai iya kalubalantar Shugaba Buhari a zaben 2019 da za ayi nan gaba, inda aka gabatar da sunayen Ahmad Muhammad Makarfi da kuma Attahiru Bafarawa domin tantancewa.

Inda daga bisani gamayyar suka amince akan Attahiru Bafarawa ya kasance wanda zai yiwa jam’iyyar PDP takarar Shugaban kasa, duba da irin ayyukan da yayi a baya da kuma yadda ya nuna gaskiya da rikon amana da tsoron Allah a yayin da ya rike Gwamnan jihar Sakkwato.

“Babu ko tantama, ana gudanar da wannan zama tsakanin kungiyar matasan Arewa da kuma wasu dattawa daga Arewacin Najeriya a Birnin-Kebbi, inda aka tattauna yadda jam’iyyar PDP zata fitar da dan takarar Shugaban kasa mai karfin da zai iya karawa da Shugaba Buhari, inda daga bisani aka cimma yarjejeniyar amincewa da tsohon Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa saboda kwarewa da kuma gogewa da yake da ita a sha’anin Siyasa da kuma Mulki.”

“Bafarawa na daya daga cikin kalilan din ‘yan siyasa masu gaskiya a kasarnan, kuma kwararren dan siyasa, wanda ya faro siyasa tun kuruciyarsa, yasan dama da hauni a siyasa, ya kuma san abinda ya dace da wanda bai dace, shi ne dan siyasa daya tilo wanda ya fara tun daga matakin kansila”

“Bugu da kari Bafarawa shi ne dan siyasa daya tilo da ya damu da hadin kai da kuma zaman lafiyar kasarnan, domin a sau da dama akan ga yadda yake nuna halin tausayi da kuma jin kai a duk lokacin da bala’i ya aukawa wasu al’umma musamman kashe kashen da ake yi na kabilanci, Bafarawa ne mutum guda tilo da kan fara kai gudunmawarsa ga mutanan da suke neman agaji”

Bayan haka kuma, Attahiru Bafarawa na daya daga cikin mutanan da aka gina jam’iyyun UNCP da ANPP da ACN da kuma APC da su, bisa jagorancinsa aka samar da jam’iyya mai mulki ta APC a Najeriya.

A lokacin da jaridar THISDAY ta tuntubi mai taimakawa Tsohon Gwamnan kan kafafen yada labarai Alhaji Yusuf Dingyadi game da wannan batu na gamayyar matasan jam’iyyar PDP da suka amince da Attahiru Bafarawa a matsayin wanda suke son ya yiwa jam’iyyar ta PDP takarar SHugaban kasa a zaben 2019, Dingyadi ya bayyana wannan batu da cewar wani abin farin ciki ne kwarai da gaske, sai dai yaki bayyana cewar ko Bafarawan zai yi takarar SHugaban kasa ko a’a.

Attahiru Bafarawa zai baiwa matasan jam’iyyar PDP amsa a lokacin da ya dace game da batun tsayawa takarar Shugabancin Najeriya a zaben 2019. Yace a yanzu haka Bafarawa ya dukufa wajen yin adduah akan Allah ya kawo mafita ga halin da kasarnan take ciki, domin samun hadin kai da kuma cigaban wannan kasar.

LEAVE A REPLY