Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya kaddara da neman shawarwari game da neman takarar Shugaban kasa a zaben 2019 a birnin Fatakwal na jihar Ribas.

Atiku Abubakar ya kuduri aniyar neman kujerar Shugabancin najeriya a karkashin tutar jam’iyyar PDP.

Taron wanda ya gudana a babban dakin taro na gidan Gwamnatin jihar Ribas, wanda Gwamnan Ribas Nsome Wike ya jagoranta. Daga cikin wadan da suka halarci taron akwai jiga jigan ‘yan Siyasa da suka hada da Okwesileze Nwodo da Abdul Ningi da su Mikel Kaase Aondoakaa da sauransu.

Mista Atiku ya bayyana aniyarsa ta ganin ya samarda sabuwar Najeriya wadda zata amfanawa dukkan al’ummar najeriya ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabila ko kuma yanki ba, ya kuma sha alwashin kawo sauyi a fannin tattalin arziki da fannin masana’antu.

Da yake magana a wajen taro, Gwamna Wike ya bayyana cewar “Atiku Abubakar ya dace ya zama Shugaban Najeriya, Shugabancin Najeriya na mutum ne da yake da tarihi mai kyau na siyasa wanda Atiku ABubakar yana da duk abinda ake nema” A cewar Wike.

LEAVE A REPLY