Shugabar ma’aikatan Gwamnatin tarayya ta ƙalubalanci Danbazau kan Maina

Shugabar ma’aikatan Gwamnatin tarayya Winifred Oyo-Ita ta kalubalanci ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau kan sake mayar da Abdulrahid Maina mukaminsa. Oyo-Ita ta ce ita sam bata bayar da wani umarni da yayi nuni da a dawo da Abdulrashid maina mukaminsa ba a ma’aikatar cikin gida da Dambazau ke zaman minsta.

Shima a nasa bangaren, Ministan cikin gida Abdulrahman Dambazau ya nesanta kansa daga batun mayar da Maina mukaminsa a ma’aikatar harkokin cikin gida ta Najeriya. Ya karyata zargin da akai masa na cewar shi ne ya bayar da umarnin a dawo da maina ma’aikatar domin cigaba da aikinsa a matsayin Darakta.

Tuni dai wasu majiyoyi suka ruwaito cewar, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya buƙaci a dakatar da baton dawo da Maina, ya kuma bayar da umarnin gaggauta bincike akan waye yake da hannu kan batun dawo da shi domin cigaba da aikinsa.

Idan ba’a manta ba, Abdulrashid Maina, ya arce daga Najeriya ne zuwa Dubai sakamakon wasu zarge zargen Almundahana ta Miliyoyin kudade akan aikin da aka bashi na kula da fanshon ma’aikatan Gwamnatin tarayya, inda rahotanni suka ce Abdulrashid Maina yayi sama da fadi da miliyoyin kudade.

Ko yaya kuke ganin yadda wannan turka turka zata kaya?