Shugaba Muhammadu Buhari daga dama, sai Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje a tsakiya, sai kuma Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu

Daga Abdulhakeem Kabir Ultrasonic

Tun bayan kasancewar shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban ƙasar Nigeria, “yan Nigeria da mutanen garin Kano sun ɗauki dogon lokaci suna jiran zuwan shugaban domin yazo ya sanya harsashin wani aiki wanda zai kawo musu cigaba mai ɗorewa kasancewar jihar tasu a matsayin bangon siyasar shugaban duk da cewa ba daga jihar ya fito ba.

Jihar Kano ta kasance jiha wanda tafi kowace jiha a faɗin Nigeria bada gudumowa wajen tara tulin kuri’u domin tabbatar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban ƙasa a shekarar 2015. Abin mamaki ne a wajen dukkan mai bibiyar lamuran siyasa idan yaga yadda shugaban yayi watsi da jama’ar jihar ta kowace irin fuska domin tun bayan hawansa mulki babu wani aiki wanda ya kawo musu.

Mafi yawan jama’a da kuma “yan jam’iyyar adawa sun daɗe suna sukar shugaban da cewa yakamata ya ziyarci jihar domin yaji kokensu sakamakon jajircewa da sukayi wajen nasarar shugaban.

Bayyanar shugaban ƙasan a jihar Kano yau ya tabbatar ma “yan Nigeria cewa yasamu naƙasu a tafiyar siyasar shi dangane da yadda jama’a suka nuna rashin kulawarsu da damuwarsu akan zuwan nashi har wasu masu fashin baƙin lamuran siyasa suna ganin zuwan tsohon shugaba Jonathan yafi armashi fiye da zuwan Buhari domin duk wanda yasan wancan zuwan nashi kafin zaɓe zaiyi mamaki idan yaga shugaban ya rasa duk waɗannan miliyoyin jama’ar a sakamakon irin salon mulkinsa wanda ya wahalar da talakawan Nigeria duk da cewa sune suka tara mishi tulin ƙuri’ar samun nasarar shi.

Da alamu dai shugaban kullun yana rasa magoya baya sakamakon irin baƙar azaba wanda talaka yakesha a mulkinsa. Da haka wasu suke ganin cewa jirgin siyasar shugaban tana dab da tarwatsewa idan bai gyara salon mulkinsa ba.

1 COMMENT

  1. Zuwan baba buhari ba campaign yazo ye ba ziyarar aiki ta kawo shi Amma duk da haka jamaa sun fito fiye da yanda ake Tasmani . Don haka wanna bayane naka bashi da toshe

LEAVE A REPLY