Daga Ado Abdullahi
Shirye shirye sun kankama a duk fadin jihar Kano tsakanin magoya bayan darikar siyasa ta kwankwasiyya, kama daga  dinka fararen kaya masu ado da ratsin ja gami da jajayen huluna masu zane- zane masu ban sha’awa. Wadansu har da tanadin takalma masu tsarin ja domin dai cikamakin kwalliya.
Shi dai madugun tafiyar tun bayan da ya mika ragamar mulkin jihar Kano ga mataimakinsa wato Dr Abdullahi Umar Ganduje a matsayin zababben gwamna, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso sau daya ya zo jihar a bainar jama’a domin jajantawa ga rasuwar mahaifiyar gwamnan mai ci. Rashin shigarsa cikin jama’a a wannan tsawon lokaci ya taimaka wajen baiwa mahukuntan jihar kwanciyar hankali domin gudanar da mulki ba tare da samun barazana daga gangamin siyasa da kan iya raba tunanin gwamnati ba.
Rashin jituwar da ke tsakanin bangarorin Kwankwasiyya da Gandujiyya kuwa, ya samo asali ne tun daga zargin da ake yiwa sabon gwamnan na kin kammala wasu ayyuka da shi tsohon gwamnan ya faro. Kwankwasawan kuma suna tuhumar bangaren na gwamna da bijirewa tsarukan darikar ta kwankwasiyya. Amma a na ta bangaren gwamnatin ta ce tana iya kokarinta wajen kammala wasu daga cikin ayyukan da ta gada, misali shi ne doguwar gadar sama da ke kan titin Murtala Muhammed a tsakiyar birnin na Kano.
Hakika zuwan kwankwaso Kano tare da yin gangami irin na siyasa ba karamin dakile farin jinin gwamnatin Kano zai yi ba, duba da yadda daman gwamnatin ba ta dade da nuna kwanjin ta wajen tara jama’ar da suka tarbi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba, lokacin da ya kawo ziyarar aiki inda ya  bude wasu manyan asibitoci da gwamna Ganduje ya kammala. Aikin da ya gada daga tsohuwar gwamnatin Mallam Ibrahim Shekarau.  Masana harkokin siyasa a ciki da wajen jihar kuwa suna hasashen da alamu jagoran na kwankwasiyya zai tara ninki yawan jama’ar da suka tarbi Shugaban kasa a wancen taro.
Matukar haka ta faru kuwa toh lallai an budawa gwamnatin jihar kasa a ido, domin wannan zai rage mata kima ba ma ga talakawan jihar ba hatta ga helikwatar jam’iyyar ta  APC da ke Habuja. Wannan kuma kan iya haskawa masu kada kuri’a wani abu, domin dai siyasar Kano mafi yawa tana karkata ne ga wane dan takara ya fi farin jini wajen tara jama’a. Domin mafi yawan matasa masu kada kuri’a yan ‘abi Yarima ne a sha kida, ba wata manufa ce ta hakika a siyasance su ke da ita ba. Irin wannan gangami na shigowa Kano ya taba faruwa a shekarar 2011, dab da shiga zaben gwamna tsakanin tsohon gwamna kwankwaso ( lokacin yana PDP) da kuma dan takarar jam’iyyar ANPP wato Mal Salihu Sagir Takai. Gangamin a wancan lokaci ya yi tasiri matuka wajen karkata akalar masu jefa kuri’a tsakanin matasan jihar inda ya sami damar darewa a kujerar gwamnan a karo na biyu. Sanin alfanun irin wannan gangami ne ya sa kwankwaso ya ke son nuna karfinsa a siyasar Kano a wannan lokaci kamar yadda ya yi a baya.
Wannan ne ya saka tsoro da firgici tsakanin  magoya bayan gwamnatin su ke ganin matukar aka bar wannan taro ya gudana to za a yi musu sakiyar da ba ruwa.
Shawara ga gwamnatin Kano shi ne ta sani in dai har wannan taron bai sa6awa kundin tsarin mulkin Najeriya ko na jam’iyyar APC ba. Ta yi ta maza ta nuna marabarta ga wannan taro domin samun zaman lafiya mai dorewa da cigaban tattalin arzikin jihar. Ta kuma ja kunnen wasu daga cikin jami’an ta da su ke kokarin tunzura mabiya domin ganin rashin nasarar gangamin. Ta tuna zaman lafiyar Kano yana gaba da komai.
Su kuma kwankwasawa su sani ‘mai kaza a aljihu ba ya jimiran as’. Su yi taro cikin tsari, nutsuwa da sanin yakamata. Ka da matasa su rudu da soyayyarsu ga wani dan siyasa ta kai su ga raunata wasu yan adawar siyasa. Su fadaku dan siyasar da ya sa ka raunata wani, gobe za ka gansu a teburi guda daya, ya sauya sheka ya hade da abokin adawarsa.
Fatan mu dai MAHADIN; kamar yadda kwankwasawa kan kira shi, ya zo lafiya, a yi taro lafiya, ya kuma koma Habuja lafiya. Amin.

LEAVE A REPLY