Bayan shekaru huɗu da hamɓarar da shi daga muƙamin gwamnan jihar Ekiti, Dakta John Kayode Fayemi yana nan yana shirin sake ɗare kujerar a ƴan watanni masu zuwa. Bayan cin nasara da ya yi a zaɓen da aka kammala tsakaninsa da mataimakin gwamna mai ci wato Farfesa Olusola Eleka na jam’iyyar PDP wanda ya sami ƙuri’u 178,129 inda shi Fayemi ya sami ƙuri’u 197,489.
Duk da dai zaɓen ya bar baya da ƙura ganin yadda masu sa-ido a harkar zaɓen suka ce an tafka maguɗi da harambe. Ita ma jam’iyyar PDP ta yi zargin an yi amfani da injin tantance masu kaɗa ƙuri’a na jihohin maƙwabtan jihar kamar jihohin Kogi, Ondo, Oyo, Ogun da jihar Lagos. Inda aka riƙa jigilar masu jefa ƙuri’a daga jihohin zuwa jihar ta Ekiti inda suka kaɗa kuri’a ranar zaɓen.  A yanzu dai jam’iyyar ta PDP ta garzaya kotu domin bayyana ƙorafinta. Daman dai kafin ranar zaɓen ƴan sandan da ake zargi sun sami oda daga Habuja sun tarwatsa wani gangami da ɗan takarar na PDP ya shirya a ranar Laraba inda aka yi harbe-harbe da harsashi mai rai aka kuma jefa barkonon tsohuwa har a gidan gwamnatin jihar.
Wannan dirar mikiya kam ta saɓa da ƴancin da dokar ƙasa ta baiwa kowane ɗan Nijeriya wajen bayyana albarkacin bakinsa da bashi damar zaɓin duk jam’iyyar da ya ga dama.
Haka kamar yadda gamayyar masu sa-ido a zaɓen na Ekiti suka bayyana zaɓen cike yake da maguɗi. Domin jam’iyyar APC ta yi magudi da nuna karfin iko wajen tursasawa masu jefa ƙuri’a da musgunawa abokan adawa gami da amfani da kuɗi ƙiri-ƙiri. Inda ta kai kafin a baiwa mutum ladan dangwala ƙuri’ar sai ya kawo shaidar hoton ƙuri’ar da ya ɗauka da wayarsa ta hannu:  wani sabon salon murɗiyar zaɓe daga APC kenan !
Tabbas Mista Fayose gwamna mai barin gado ya san haka za ta kasance domin gwamnatin tarayya dole ne za ta karɓi wannan yaƙin, ba za ta zura ido ya cigaba da yi mata cin kashi da nuna baƙar adawa  ga Shugaba Muhammadu Buhari ba. Daman mun san a rina kuma dole ne gwamnatin tarayya  ta murɗe wannan zaɓe. Babu mamaki ganin yadda aka antayo ƴan sanda wajen 30,000 wai domin kawai bayar da tsaro ga jihar.
Abin da wannan zaɓe dai yake nunawa shi ne har yanzu jama’ar jihar Ekiti suna da ruhin jam’iyyar PDP a jikinsu domin duk da angizo kuɗi daga Habuja jam’iyyar ta sami cin kashi 47 cikin 100 (47%) inda aka ba ta tazarar ƙuri’u kusan 19,000 kacal.
Hakanan dai farin jinin shugaba Buhari da ake kurantawa bai sami wani tagomashi ba domin dai sai da aka yi amfani da kayan aiki. Sayen masu jefa ƙuri’a da kuɗin da suka tasamma naira 3,000 har zuwa 10,000 ba ƙaramin abin kunya bane ga gwamnatin tarayya wacce  take ganin farin jininta ne zai ba ta nasara.
Hakanan wannan yana nuna rauni da kuma ƙalubalen dake gaban jam’iyyar APC ta ƙasa a zaɓen 2019 dake tafe. Saboda bai kamata a ce a yankin Yarabawa sai jam’iyyar ta sayi ƙuri’a da  kuɗi da amfani da ƙarfin iko daga Habuja kafin ta ci zaɓe ba. Domin ƙasar Yarabawa nan jam’iyyar APC ta fi ƙarfin faɗa a ji, kuma a  gurin da aka yankewa jam’iyyar cibiya tun tana ACN.
Wannan tafka maguɗi mun iya cewa ba ta dai sake zani ba, ko mu ce duk dai kanwar ja ce. Domin duk iƙirari da kirarin da ake yi wa jam’iyyar ta APC a matsayin masu kawo Canji a tsarin siyasa da kawo cigaba ga al’ummar ƙasar nan zancen banza ne kawai. Abin da suke zargin jam’iyyar PDP da shi su ma sun aikata hakan.
Ado Abdullahi

LEAVE A REPLY