Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar
Allah Ka jikan dukkan Wanda ya ran sa a kashe karshen rayukan da ya zama Ruwan-dare a jihar Zamfara; Wanda, mafi yawan lokaci talakawa ya ke Shafa. Ya Allah Ka yi mana maganin wannan mummunan zalunci, Ameen.
Babban abin takaicin a wannan al’amarin shi ne yadda masu mulki suka yi biris, su ke nuna halin ko in kula a kashe karshen da ake yi Akan al’ummar Musulmi. Na tabbatar da Kirista su ke fuskantar wannan, da watakila yanzu babu Nijeriya. Ya Allah Ka wuce mana GABA, Ya Allah Ka dubi rashin gatanmu Ka gaggauta Saka mana, Ameen.
BUGU da Kari, ko labarin da kafofin sadarwa za su bayar Akan Kisan, sai Ka taras Ba Kai Ba gindi; an kudundune labarin ta sigar da Ba za a iya fahimta Ba! Yanzu har ta Kai mun fahimci cewa Idan Ba a son a fahimci daga wane addini Mai kisa ya fito, sai a lullubeshi da wani suna Na ALMARA, ko a kirashi: “gun man”, ko bandit, ko armed man! Amma da Zaran ta tabbata Musulmi ya aikata, to a nan, addininsa sai ya bayyana. Wannan wulakanci ne, cin mutunci ne da kuma tozartawa!
ME YASA AKE YAWAN KASHE KASHE A ZAMFARA?
Jihar Zamfara kasa ce ta noma, Mai dimbin arzikin maadinai masu tarin yawa. Watakila Ana hasashen Duk Afrika babu wani yanki da Allah Ya Ba arzikin maadinai Irin jihar Zamfara.
Ta tabbata a yanzu, cewa daga wata kididdiga da gwamnatin Tarayya ta gudanar Akan albarkatun maadinai Na kasar Nijeriya, an gano cewa jihar Zamfara tana da Kusan dukkan Maadini 34 da duniya ta ke bukata domin sarrafawa. Amma sai gashi a yau, jihar Zamfara tana a Sahun GABA Na jihohin AREWA da suka yi fice wajen talauci. Wannan al’amari yana da ban mamaki; arzikin kasar noma bai arzuta jihar Zamfara Ba, kuma yawan maadinai bai wadata ta Ba; kullum sai Kisan ‘ya’yanta a ke yi? Me nene dalili? Ina masu mulkin Zamfara, Ina manyan maikatan Jihar Zamfara Na koli, Ina Janar Janar Na ta Na Sonja, Ina manyan malamanta, hasali Ina manyan YAN BOKONTA? Jama’ah a duba maganarka nan, a binciki al’aman nan, akwai lauje cikin Nadin!
Tun lokacin da aka samo zinari garin Maru, Irin wadannan kashe kashe Na gilla suka samo Asali. Ba abin mamaki Ba ne samuwar maadinai ya janyo kashe kashe musamman Idan muka yi la’akari abinda ya ke faruwa a kasar Dimukradiyya ta Congo; amma abin mamakin shi ne yadda manya suke biris da wannan mummunar Annoba!
Masu lura da abubuwan da ka-Je-su-zo, sun yi Bayanin Irin yadda duniyar Turawa ta dau dumi a lokacin da jihar Zamfara ta qaddamar da Shariah a shekarar 2003. Wani Babban Masani, Mai Bincike, kuma Sheihin Malami Gangaran, watau Farfesa Ali Mazrui, ya Fadi cewa, wannan kaddamar da Shariah da jihar Zamfara ta yi, shi ne Karo Na farko da wata nahiya da ta zauna karkashin mulkin mallaka ta taba lakuce wa Bature hanci  tun bayan lokacin da Turawa suka bar mulkin mallaka! Ko wannan ya iya zama dalili?
Na yi Bincike Mai zurfi Akan wa ya kamata in tattauna da shi Wanda Zai iya kawo dauki? Sai aka sanar da ni cewa, Maigirma Senator Kabiru Marafa, shi ne Wanda ya kamata. Ina fata wannan tsokaci nawa Zai Isa gareshi kuma ya share wurin tattaunawar da zata amfani ‘yan uwanmu da AKE bi gida gida Ana kashewa Kamar Kaji. Wallahul Musta’aan!

LEAVE A REPLY