Daga Ado Abdullahi

Tabbas kiran ku da sunan Ƴan Buhariyya aqidah ya yi daidai domin abin naku ya wuce haƙiƙanin fahimta irin ta siyasa ya zama wani abin daban. Domin shi wanda ya ke bin aqidah kowace iri ce, baya ganin kuskurenta illa kullum ganin daidanta. Dole ne mutum dan Adam wanda ba ma’asumi bane wato ba Annabi ko Manzo ba, a same shi da kurakurai wajen aiwatar da al’amuransa domin ba daga Allah yake samun umarni ba.

Buhari dan Adam ne kamar kowa wanda kawai a zahiri ake kyautata masa zato na mutumin kirki, gaskiya da riƙon amana wanda wannan siffa kuwa ana samun ta daga wasu waɗanda suka gabata, ko suke raye a yanzu da kuma nan gaba, domin mu ba mu fidda tsammani daga rahamar ubangiji ba.

Kuma kasancewar mutum mai gaskiya kawai ba ita ce ta ke bashi lasisin ba zai yi kuskure ba, ba kuma shi kaɗai zai iya jagorantar al’umma ba. Shi shugabanci bayan gaskiya da rikon amana ana son mutum lafiyayye mai kaifin basira, masanin rayuwar yau da kullum, masanin siyasa da kuma tsausayi ga al’umma.

A baya an yi shugabanni a ƙasar nan waɗanda suka nuna amana haɗa da basira da iya mulki fiye da Buhari, sun zo kuma sun shuɗe. Fatan mu Allah Ya rahamshe su. Kenan idan ma mun ƙaddara Buharin bayan gaskiyar yana da ƙwarewar mulki toh shin bayan ya kau shikenan babu sauran wanda ya cancanci riƙe ko jan ragamar ƙasar nan? Domin a cikin ƴan Buhariyya aqidar akwai masu iƙirarin cewar babu mutumin kirki duk faɗin Najeriya sai Buhari. Toh shin kenan bayan wucewar Buharin wa kuma za ku kama tun da kun bar tsarin Allah kun kama na mutum ?

Mun ga mulkin Buhari na baya (1983-85) ya yi ya gama babu wani abu na raya ƙasa da cigaba da ya tsinanawa ƙasar nan domin rashin kyakkyawan tsarin tattalin arziƙin ƙasa. Haka a wannan babin tabbas mulkin Buhari ya gaza da biyawa milyoyin al’ummar ƙasar nan da suka zaɓe shi buƙatunsu, inda wasu shafaffu da mai kaɗai ne suke wadaƙarsu kamar yadda ake yi a baya. Kuma babu wanda aka hukunta bayan an kama su dumu-dumu da tafka laifin cin amanar ƙasa. Jami’an gwamnati da suke riƙe da wasu muƙamai suna karɓar cin hanci da rashawa babu ƙaƙƙautawa. Ƴan majalisu suna kwasar albashi da alawus da yafi ƙarfin buƙatunsu bayan ga gwamnatocin jihohi da dama sun kasa biyan talakawan ma’aikatansu ɗan albashin da bai taka kara ya karya ba.

A ɓangaren tsaro kuwa, masu tayar da ƙayar bayan da ake cewa an kawo ƙarshensu har yanzu basu daina kashe al’umma a kasuwanni da masallatai ba, haka basu bari an buɗe hanyoyin tafiye-tafiye a wasu gurare a arewa masu gabashin ƙasar nan ba. Hatta kame ƴan matan sakandaren Dapchi ya nuna gazawar gwamnatin Buhari a kan tsaro. Kame mutane domin a ƙarɓi kuɗin fansa ya zama kamar ma yanzu aka fara a ƙasar nan.

Rigingimun makiyaya da manoma abin kamar almara, ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Kuma wannan duk ƙarƙashin mulkin Baba mai gaskiya. A shiga ƙauye guda a kashe mutane sama da ɗari a Zamfara ko a Birnin Gwari na jihar Kaduna ya zama ruwan dare duk a idon jami’an tsaro ƙarƙashin wannan gwamnatin ake aikatawa. Faɗace-faɗacen ƙabilanci a jihohin Binuwai da Taraba ya ƙi samun sauƙi. Ƴan fashi da makami suna addabar al’umma a gida da hanyoyin mota. Abin fa ba zai lissafu cikin sauƙi ba.

Idan ka dawo ɓangaren tattalin arziƙi abin ba a cewa komai. Nan ne talaka yake cin ƙwal ubansa, domin abin da zai kai bakinsa ne ma ya ke gagararsa. Kayan masarufi tun hawan wannan gwamnati suke tsula tsadar tsiya duk saboda sakaci da rashin kyakkyawan tsarin da za a ɗora tattalin arziƙin ƙasar a kai. Rashin aiki sai ƙaruwa yake bayan kuma cikin alƙawurran wannan gwamnati akwai samar da aiki ga matasa kusan milyan uku duk shekara. Amma sai aka sami akasin haka.

Kamfanoni kullum sai ƙarin haraji su ke samu daga gwamnatoci maimaƙon a ba su yanayi mai kyau domin kawo cigaban ƙasa. Batun shawo kan matsalar samarwa da raba man fetur ya gagari gwamnati domin har ta kai sun koma tsarin gwamnatin baya na bayar da tallafi ga masu shigo da man. Tsarin da an tabbatar cike ya ke da muguɗi da kwarafshin. Abin da Buhari a baya ya ce ba zai lamunta da shi ba bayan ya hau mulki.

Toh duk fa waɗannan kurakurai da aka kasa shawo kansu ƙarƙashin mulkin ƴan kawo canji, shi ɗan Buhariyya aqidah ya rufe idonsa baya ganin su. Shi a wurinsa duk abin da Buhari ya yi daidai ne kamar dai wani da aka aiko da saƙo daga sama.

Shi ɗan Buhariyya aqida duk wanda ya saɓawa Shugaba Buhari a fahimta, to ya zama kamar wani ƙaramin kafiri. Babu dama ka soki jam’iyyar APC ko wannan mulkin mai cike da tufka da warwara da tsabagen alƙawurra da babu cikawa sai ƴan ƙorensu ko ƴan jagaliyarsu sun bi ka da zagi.

Ɗan Buhariyya aqidah ya kamata ya san kima da daraja da mutuncin ƴan adawa ga mulkin dimocraɗiyya. Shi ɗan adawa ba maƙiyi bane ga masu mulki, illa kawai wata fitila ce wacce ta ke haskawa shugabanni domin su hararo inda suka yi kuskure domin su gyara. Ya kamata su sani yadda kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya basu damar kwarzanta gwaninsu haka tsarin mulkin ya baiwa ɗan adawa damar suka mai ma’ana ga kowaye a bisa mulki.

A ƙarshe ina nasiha ga ƴan Buhariyya aqida da su mayar da siyasarsu ta zama ta manufa ba ta “ko a mutu ko ayi rai” ba. Kada su tsuke tunaninsu ya zama siyasar goyon bayan mutum guda ba tsarin jam’iyya ko manufarta ba. Su buɗa ƙirjinsu wajen ji ko karanta abin da wasu masu ganin ba a yin daidai za su faɗa ko su rubuta da ya saɓa da manufar gwanin nasu. Rashin haka shi ke tunzura wasu masu kaifin tunani daga cikin magoya baya suke ta dawowa daga rakiyar tafiyar Baba Buhari. Domin yanzu yadda ake sauka daga tafiyarsu abu ne a fili magoya bayan Buhari raguwa suke ba ƙaruwa ba.

LEAVE A REPLY