Daga Mahmud Isa Yola
A rubutun mu da ya gabata, mun karanta falala da ke cikin Azumi inda muka tsakuro Hadisai guda 12 muka fassara. Bayan falala da Azumi ke dauke da shi, akwai amfani ko ince ribar da mai azumi yake kwasa, Kamar yadda yazo cikin Ayoyi da Hadisai.
Farko dai azumi yana sanya takawa (jin tsoron Allah) kamar yanda yazo a karshen ayan nan da yayi magana a kan azumi na Suratul Baqara aya ta 183. Malaman tafsiri irin su Abdullahi Dan Abbas sun bayyana cewa, abunda ake nufi da lafazin “la’allakum tattaquun” shine, muddin mutum zai iya kamewa daga abubuwa na halal (ci da sha da kusantar iyali) don ya samu dacewa a wurin Allah SWT kuma ya tsira daga azabar Sa, to mutumin da zai yi wannan, kamewa daga haram ba zai bas a wuya ba.
Haka kuma idan mai azumi yaji radadin yunwa yayin da yake azumi, zai kara fahimtar yanda miskinai suke fama, wanda sanadiyyan hakan na iya kara jinkan miskinai a zuciyar mai Azumi wajen ciyar da su.
Azumi ishara ne ga duniya akan hadin kan musulmi. Dukkan musulmi, masu dukiya, talakawa, kabilu daban daban suka suna haduwa a aiki guda kuma a lokaci guda: yin azumi.
Azumi babban dama ce ga mumini na samun gafarar Ubangijin sa. Yazo cikin hadisi Manzon Allah SAW yace “Duk wanda ya azumci watan ramadaan da imani tare da yakinin samun yaddan Allah, za’a gafarta ma sa dukkan zunuban sa da suka gabata. [Bukhari, Fat’h 37]
Haka kuma Azumi na koyar da rai yanda zata bi da sha’awa. Sawa’un sha’awa ta dukiya, ko jinsi, ko wani abu na duniya wanda watakila ma ta hanyar Haram ce zai iya biyan wannan bukata. Sanadiyyar kamewa da mutum yayi a Ramadaan, in Allah ya datar da shi sai kaga ko bayan Ramadaan ma zai iya kamewa Insha Allah.
Allah SWT ya sa mu dace, Amin.

LEAVE A REPLY