Abbas Yushau

Me yasa Gwamnatocin baya suka fi na yanzu ayyukan raya kasa da al’umma suke amfanar sa har zuwa yanzu?

Babban misali da zan bayar shi ne jahar mu ta Kano inda anan ne nafi wayo, Marigayi Audu Bako ya gina madatsar ruwa ta Tiga amma har yanzu kusan kimanin shekara hamsin manoma na amfanar wajen saboda wannan kyawun aiki ne yasa Gwamnatin tarayya ta karbe wannan madatsa ta Tiga.

Kuma a wancan lokacin kudaden Shiga na Gwamnatoci basu kama kafar na yanzu ba.

Tun dawowa mulkin Dumkradiyya a Shekarar 1999 babu Gwamnatin data warware matsalar ruwan sha na famfo a Birnin Kano da kewaye, har yazuwa yanzu tsirarun Unguwanni ne suke da ruwan famfo, a yanzu yakin neman zabe na ”yan siyasar jihohi ya fara tashi daga zan sama muku ruwan sha ya koma wasu abubuwa daban.

Allah ya jikan Marigayi tsohon Gwamnan Kano Muhammadu Abubakar Rimi, sanda yana mulkin tsohuwar jahar Kano da Jigawa yayi ayyukan da har yau alummun wadannan manyan jihohi na amfanarsu, daga ciki akwai gidan Talabijin na ARTV da kamfanin jaridar Triumph da makarantun sakandire da ya gina fiye da dari biyu a jihohin Kano da Jigawa.

Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ya kai ‘yan asalin jihohin Kano da na Jigawa karatu kasashen wajen da suka hada da Bulgaria domin su karanci aikin likita da sauran fannoni na rayuwa, kuma a wancan lokacin na zamanin su Marigayi Rimi babu TEN Percent na Gwamna da kwamishinoninsa ida sun yi kwangila, kuma ga aiki nagartacce.

Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ta kai idan yazo wucewa ta wajen Unguwar Farm centre sai yayi kamar zai yi kuka ,domin ya shirya yin kasuwa ta zamani mai kyau da tayi dai dai da World Trade Centre ta Newyork ,amma sauran Gwamnatocin soja da suka gaje shi suka yi shakulatan bangaro da abun,su kai ta shata filaye babu kakkautawa,gurin ya zama bashi da tsari, kuma duk ya gudanar da ayyukan raya jahar Kano da Jigawa ne a takaitaccen shekaru hudu da yayi.

Amma yanzu me ke faruwa Gwamnatocin jihohin kasar nan da na tarayya sai shaci fadi, da alkawarurrukan da basa cikuwa.

Maimakon shugabannin yanzu su dauki matsala daya su yi maganinta ko a shekaru hudunsu na farko ne basa yi. Yanzu kalli babbar matsalar da bangaren lafiya ke fuskanta na rashin wadatattun asibitoci da gadajen kwanciya, ga matsananci rashin yanayi mai kyau na koyo da koyarwa.

A yanzu labari da yake isheni cewa akwai makarantun sakandire a jahar Kano da ake da dalibai 300 a aji da ma dai sauran matsaloli da basa misaltuwa.

LEAVE A REPLY