Daga Anas Saminu Ja’en G/Makera, Kano

Haka abun yake a yankin arewacin Najeriya da zarar an ce zabuka sun fara gabatowa kai ta ganin gungun ‘yan uwa masata da kayan maye ko kuma muggan makamai, Kamar yadda kuke gani cikin wannan Hotunan da suke ta yawo a shafukan sada zumata, An ce wai magoya bayan Sanata Kabiru Gaya ne dauke da Sanduna da Barandami a lokacin da suka zo tarbar wakilin na su koma dai menene.

Sai yaushe ‘yan uwa matasa ‘yan talakawa a kasar musamman a yankin mu na Arewa za mu gane cewar mu ya mu muke bin ‘yan siyasa da muggan makamai kuma muke raunata kan mu, hatta musayar kalaman batancin ga junan mu, su wadanda muke yi domin su, idan sun gamu a tsakanin su, haka zaka ga sun rungumi juna suna cin abinci tare, su shiga daki su kulle kofa su bar mu.

Misali: ko a wannan masu makaman babu d’an shi Kabiru Gayan babu wani d’an uwansa na jini, Duk fa wadannan ‘yan siyasar da muke bi ‘yan uwa matasa tini sun shiryawa iyalan su rayuwa mai kyau ko bayan ba ran su, mu kuma an dora mana dakon jahilci da hauka muna kin junan mu tare da raunata kammu saboda siyasa kuma ita siyasa tana karewa amman mutunci baya karewa, yaushe za a ce wai shugabannin da muka zaba muke saran za su kare mana lafiya, dukiyoyin mu tare da ba mu gudunmawa wajan ba mu ilimi ingattacce kuma sune suke bamu kwayoyi da makamai domin mu rage kammu da kammu saboda sun daukemu wawaye gaskiya ya kamata matasa mu yi karatun ta nustsu.

Ko sai yaushe wasu daga cikin ‘yan uwa matasa magoya dayan ‘yan siyasa zasu gane gaskiya su yi karatun ta nutsu?

LEAVE A REPLY