Wakilin gidan radiyo freedomAbbas Yushau
Daga Abbas Yushau
Babban Kalubalan da Shugabannin Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci shi ne kafofin sada zumunta da suka hada da Facebook, Twitter da Whatsapp, Instangram da sauransu .
Tunda aka shiga wahalar man fetur a kwanakinnan, babban abunda zai baka shaawa shi ne yadda kowa yake bayyana raayinsa da rashin jin dadinsa game da irin kwalawar da jamaa suke yi akan karancin man fetur.
Yanzu daya daga cikin nasarar da zaa samu musamman a Arewancin Najeriya shi ne mutanan mu na karkara da masu kananan sanaoi da ya hada da masu garuwa, Yan Tula ,masu kifi ,masu hakar rijiya ,da sauransu su sanin amfani SOCIAL MEDIA kamar yadda wadanda sukai ilimin boko suka kai har sakandire suka  samu, wannan zai sa dan Najeriya ya kara samun wayewa ta yadda ake mulkarsa.
Na tabbata yadda kullum ake samun kalubale ta Facebook da Twitter idan mafiya yawan yan Najeriya da basu damu da harkar ba suka shigo ,to juyin juya hali ya taho kamar na Tahrir Square da ya faru a shekarar 2011 watan Fabrairu a kasar Misra ya kawo karshen mulkin Hosni Mubarak.
Kasar nan ta shiga matsaloli iri daban daban, amma da zaka karanta littafin Iliya dan Mai Karfi zaka san cewa bamu shirya gyara kasar nan ba, Kalli yadda ILIYA DAN MAIKARFI ya gagari kowa ya kawo canji duk da cewa kirkirarran labari ne ,amma har yanzu ina tuna sanda nake takarar littafin ILIYA, daga shi sai dokin sa Kwalele amma sai da ta kai Iliya shi kadai ya kori mayaka babu adadi daga Birnin Kib har zuwa garin Kanifo ,ta kai Gogaji da yake tare fatake ya toshe hanya shekara hamsin baa bi, da Iliya ya sakar masa kibiya ta kunne sai da a ka rika mamaki, kai a wannan lokaci sai da Gogaji ya nemi ya bawa Iliya cin hanci na mallaka masa duk dukiyarsa amma Iliya dan mai karfi yace ba zai yiwu ba.

LEAVE A REPLY