Yayin da Shigaban kasa Muhammadu Buhari yake sanya hannu akan kasa kudin shekarar 2918
Daga Muhammad Sulaiman
Budget: In an bi ta barawo, sai a bi ta mabi-sawu, in ji Bahaushe. Duk sun rikita lissafin kasafin qasa. Wannan ya ce kaza, wancan ya ce kaza. Dadinta dai duk Allah Yana kallon su. In mu kun raina mana hankali, da sannu za ku gamu da masu casa ku a gidan gaba. Najeriya akwai cukurkudedeniya. Allah muke roqo ya taimaki masu gaskiya.
To wai da wa za mu yarda game da kasafin kudin nan? Galibin talakawa dai mun fi yarda da Baba Buhari, to amma na ji ana rawaito wasu maganganu da ya kamata fa a duba. An ce kudin aski shugaban qasa da muqarrabansa kawai sun kai kusa miliyan 57! Wane irin gashi ne da su haka?
Haka nan mun ga an ware wasu maqudan biliyoyi don sabunta ginin United Nation a Abuja, amma ‘yan majalisa sun mayar da shi miliyan 100. Ina ganin kamar a nan sun yi daidai.
Sai kuma maganar airport ta Enugu inda aka ce tuni an fitar da biliyan 1.7 kamar yadda minista Hadi Sirika ya fada daga cikin biliyan 2 da aikin yake buqata. Amma sai ga shi an qara kai wa majalisar qasa biliyan 2, bayan abin da ya rage bai fi miliyan 300 ba. Su kuma suka mayar da shi miliyan 500.
Wato in ka tsaya ka duba abubuwan a cikin tsanaki, suna da dan rikitarwa. Da yawa dai mun fi kyautatawa Baba zato, don haka ba ma tsayawa mu yi duba zuwa ga matsalolin da ka iya tasowa daga bangarensa, alhalin muna da masaniyar yana dabaibaye da wadanda ba sa son ci gaban qasa a tare da shi, kuma ya kasa yi musu komai.
Mu dai mu gani a qasa kawai. Amma wadannan lissafe-lissafen naku, ku kuka sani. Mu gani a qasa kawai. Kullum sai bajet ake yi ana baje koli da watandar kudin qasa, shi kuwa talaka sai qara baje shi ake yi. Allah Ya taimaki masu gaskiya.

LEAVE A REPLY