Farfesa Farooq Kperogi

Da dama ana zargin rubuce-rubucen da na ke yi, musamman na baya-bayan nan game da yanayin yadda shugaba Muhammadu Buhari ke tafiyar da mulki cikin rashin kwarewa, ina yi ne saboda tsammani na akan Buharin ya yi yawa ta yadda na ke bashi wani iko da karfi sama da yadda ya kamata mutum ya tsammata daga wajen wani mutum. Wasu na ganin ma, ina yi Shugaba Buhari ganin ba zai yi kuskure ko rashin dai-dai ba tamkar ba mutum ba. Duk mai wannan tunani game da ni, ina mai fada masa cewa wannan kuskure ne ko shakka babu.

La’akari da sadarar farko ta kasidar da na rubuta a ranar 16 ga watan Mayun 2015 (kwanaki 13 kafin Shugaba Buhari ya karbi mulki) mai taken “6 Reasons Why Incoming Buhari Government Fills Me With Hope”, ma’ana: (Dalilai 6 Da Suka Saka Nake Kyautata Zato Ga Gwamnatin Buhari). A cikin sadarar na bayyana cewa gwamnatin Buhari ba za ta zama dari bisa dari bata da aibu ba. Za ta yi dai-dai a wani bangaren, a wani bangaren kuma za ta yi kuskure. Za ta yi abubuwa da suka saba da burika da kudirorinmu. Za ta saba mana. Za ta bamu haushi. Amma, ina da yakinin cewa wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari za ta zo sabon salon yanayin gudanar da gwamnati da babu wasa ko cin amana da rashin kwarewa a ciki. Gwamnatin da za ta kakkabe ‘yan bangar jami’an gwamnati.

A saboda haka, bani da wani tunani ko a baya can na cewa Buhari ba zai yi kuskure ba, domin kuwa na san shi ba ma’asumi bane, kodayake dai ina da zato kyakkyawa game da shi saboda yanayin yadda ya baiwa ‘yan Nijeriya wani tunani na musamman game da shi a matsayin wanda ba gama-garin dan Nijeriya ba. An fara gwamnatin nan ina cike da fatan cewa ko dai Buhari bai zama 9 ba tunda babu yadda za a yi ya zama 10, to, zai zama akalla 8. Ta yadda za mu iya cewa “Buhari 8 ya ke bai cika 10 ba.” Amma kash! Sai gashi Buharin da mu ke kyautatawa zato shi ne ya keta mutunci, muhibba, daraja da kimar gwamnati da shugabanci sama da duk wani shugaba da aka taba yi a kasar nan.

Ga dalilai na:

 1. Ya dauki Shugaba Buhari kusan wata 6 kafin ya kafa majalisar zartarwarsa. Bamu taba samuun gwamnati a Nijeriya da ta dauki adadin wannan lokaci bata nada ministoci ba. Abin takaici, bayan duk tsowon wannan lokaci da ya shafe, sai ya nada mutanen da basu da wata kima a idon ‘yan Nijeriya.
 2. Ya dauki shekaru uku kafin ya nada shugabanni da mambobin hukumomin gwamnati wadanda sune sitiyarin da ke juya akalar kowace gwamnati. Wannan ko shakka babu ya sanya gwamnatin Buhari ta ke a daskare babu uhm babu uhm-uhm. Komai ya tsaya cak.
 3. A mulkin Shugaba Buhari ne aka fara baiwa matattu mukami. Wasu da dama daga cikin mutanen da suka samu mukamai ba a tuntubesu ba aka basu.
 4. Shugaba Buhari babu ruwansa da yin jawabi ga al’ummar Nijeriya daga lokaci zuwa lokaci. Muna samun jawabi ne kawai daga Buhari in baya gida Nijeriya.
 5. Babu ruwan Buhari da ziyarar inda aka samu ibtila’i da ya yi sanadiyyar rayuka da sarar dukiyoyin jam’a kuma bai damu da ya yi jawabin jaje ga wadanda abin ya shafa ba.
 6. ‘Yan Nijeriya basu san dadin gwamnatin Buhari ba sai da mataimakinsa Osinbajo ke rikon kwarya a lokacin da ya ke jinya a Landan.
 7. Buhari ya gaza nada kwararru akan tattalin arziki a kwamitin tattalin arziki na kasa, sai ya buge da nada wanda ya kware a harkar jakadanci a matsayin mashawarci kan harkar tattalin arziki, sannan ya tura aikin tattalin arzikin kasar zuwa ga ofishin mataimakin shugaban kasa.
 8. Buhari ya nuna bangaranci a wajen nade-nadensa, inda ya fi baiwa bangaren da ya fito wato arewa muhimmanci a nade-nadensa bayan kuwa kasar Nijeriya baki daa ce ta zabe shi.
 9. Gwamnatin Buhari na yin karyar rainin hankali ga al’ummar Nijeriya har akan abubuwan da gaskiya ta bayyana garesu.
 10. A ware biliyoyin Naira wa asibitin fadar shugaban kasa a kasafin kudin Nijeriya, amma hatana mai dakin shugaban kasa da ‘yar cikinsa sai da suka koka kan yadda asibitin ke fama da kamfar kayan aiki da magunguna. Shi kansa Buhari sai da ya fita kasar waje don a duba lafiyarsa.
 11. Jirar dalili komai kankantarsa na ya shilla ya bar kasar nan. Kullum Shugaba Buhari a tafiye ya ke.
 12. Shugaba Buhari ya yaudari ‘yan Nijeriya ta hanyar nuna musu duk daya muke a wurinsa, amma a aikace yana bambanta mu musamman ma ta yanayin yadda aka bashi kuri’a a lokacin da aka zabe shi
 Abin takaici kuma har wasu da suka amfana da gwamnatin ko kuma wadanda suke son Buhari a matsayinsa na Buhari suna mana fatan ya ci gaba har zuwa bayan 2019. In wannan shi ne muradin ‘yan Nijeriya, to, bani da ta cewa, amma maganar gaskiya ita ce “Baba ya gaza” ta kowane fanni na shugabanci da jagoranci, kuma ya ragargaza darajar tafiyar da gwamnati.

LEAVE A REPLY