Daga Ayeesh A. Sadeeq

ayeeshasadeeq2010@gmail.com

Shaye-shaye ya zama ruwan dare a tsakanin matasan wannan zamanin, abin al’ajabi da mamaki bai wuce yanda gaba daya jinsin wato maza da mata ke tu’ammali da kayan maye.

Da yawan su hakan ya faro asali ne daga abokan da su ke mu’amala da su. Mafi yawancin iyaye da malamai na matukar kokari wajen ganin sun nuna ma matasa illar da ke tattare da shaye-shaye. Sai dai akan yi rashin sa’a da wasu iyayen da ke bada gudunmuwarsu wajen lalacewar yaransu.

A matsayinmu na matasa akwai buƙatar mu san wadanne abokai ya kamata mu yi hulda da su, kamar yadda bature ke cewa “Show me your friends and I’ll tell you who you are”. Wasu zasu taso da kyakkyawar tarbiyya, sai dai kash! Abokan da suke haduwa dasu kan gurbata wannan kyakkyawar tarbiyya.

Akwai matsalar nan ta da yawan iyaye basu damu da sanin abokanan ƴaƴansu ba, idan aka yi rashin sa’a sai yaran su hadu da abokanan banza, daga nan halayensu na kwarai kan canza.

Wasu daga cikin yaran kan iya bakin kokarinsu wajen ganin sun nusar da abokansu illar shaye-shaye da suke yi, sai ayi rashin sa’a abokan sun yi nisan da ba sa jin kira. Maimakon wadancan na kwaran su rinjayesu sai na banzan su rinjaye nagari, shi kenan sai su taru su zama daya.

Babu dalilin da zai sa ka yi mu’amala da mutumin banza, idan ya zama dole to ka nisance shi sai idan akan abin da ya zama dole ne, hira tsakaninku ta zama ragagga.

A matsayin ka na matashi babu amfanin ka sha abinda zau gusar ma da hankali, ya sa ka fita hayyacinka, dadin da za ka ji na kankanin lokaci ne, amma illar da hakan zai haifarma har karshen rayuwa ne. Ka zubar da mutuncin gidanku, da naka. Ka bata rayuwarka a banza a wofi, ka zama ja baya a cikin abokanan ka, watakila kuna aji daya dasu a dalilin shaye-shaye su wuce ka a karatu, wasu har su cimma burinsu, kai ba ka tsinana ma rayuwarka komi ba.

Sannan ita kanta gangar jikinka a cikin hadari take, gaba daya za ka canza lafiya za tai maka karanci, banda yiwuwar rasa hankalinka kacokam a kowane lokaci ba tare da notis ba.

Daga lokacin da ka fada shaye-shayen miyagun kwayoyi daga lokacin kayi maraba da miyagun halaye, kadan daga cikinsu akwai sace-sace saboda kudin da za ka yi amfani da su wajen siyen kayan maye.

A duk inda ka san za ka zauna ya zama cikin mutanen kwarai ka ke zaune, sannan ka sama zuciyar ka tsanar shaye-shayen miyagun kwayoyi, sannan ka san irin abokan da za ka yi hulda da su, ko da ka ji sha’awar yin hakan ka tabbatar ka kaurace ma hakan.

Sannan iyaye ku sa ido akan ƴaƴanku, su waye abokanan su, ina suke zuwa. Wasu iyayen na da matsalar ƙin yarda da ƙarar da ake kawowa na yaran su. Wasu zasu nuna cewa an yi ma yaransu sharri basa shaye-shaye, akwai wadanda ke daukar cewa yaransu ba shaye-shaye suke yi ba asari ake ma su, ko kuma aljanu ne ke shafarsu.

Ya kamata iyaye su hankalta duk inda mutum daya, biyu, uku zai kawo ma shaidar danka ko yarka to ka bincika ks gano gaskiyar zancen ta hakan za ka daƙile abin. Amma daga zaran kayi kunnen uwar shegu da lamarin, daga lokacin ne yaran zasu yi kamari akan mummunan abun da suke yi har ya zamo ba za ka iya shawo kan abin ba.

 

LEAVE A REPLY