Daga Mahmud Isa Yola

Fitinannen shugaban kasan Amurka, Donald Trump ya siffanta shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari da kalmar ‘lifeless’ ma’ana shi ‘tamkar gawa ne’ mara kuzari.

Duk da cewa duniya ta shaidi Trump da tsantsan katobara, tsangawama da tsaurin ra’ayi, akwai manufa da Trump yake da shi na muzanta shugaba Buhari.

A nazarin Trump, Shugaban kasa Muhammadu Buhari shine shugaba na farko, tun bayan da mulki ya koma hannun farar hula a shekarar 1999 a Nijeriya, wanda bai da kadara na biliyoyin daloli a turai. Buhari shine wanda makiyan sa, masu sukan sa da masoyan sa suka shaida baya shan giya, ko neman mata, ko tsafi –daga abun da suka bayyana daga gare shi.

Tun bayan da Trump ya bayyana aniyar sa na tsayawa takaran shugabancin kasar Amurka, hotunan sa na fitsara da mata suka yi ta bayyana. Mutum ne mai tsananin bushasha a rayuwar sa, wanda zai yi komai saboda biya wa kan sa sha’awar zuciyar sa.

Irin wannan rayuwa shi ne Trump yake nema a wurin Buhari, kuma bai samu ba. Wannan yasa yake kalubalantar sa.

LEAVE A REPLY