Sheikh Aliyu Said Gamawa

Muna kwana muna tashi da sannu har zamu iso ranar mu ta karshe. Tabbas wata rana sai labari. Don kamar yadda muke barci muke farkawa haka wata rana  zamu koma ga Allah kuma a tashe mu don hisabi.

Kamar yadda kowa ke fatan farko da karshen rayuwar sa yayi kyau haka ake so mu himmatu wajen shuka alheri a rayuwar mu. Ita fa rayuwa tabbas tana da Iyaka.

Haka nan duk yadda ka Kai ga isa ko gazawa akwai ranar da zaka sa tufafi azo a cire maka don wankan karshe, a maka likkafani kan hanyar ka ta zaman kadaici a kabari.

Shi kabari masauki ne da ba tsanani ba dadi sai halin ka da aikin ka da kaje dashi. Irin wannan yanayi da kowa zai shiga yau ko gobe yasa nake tuna mana cewa mu dage wajen rayuwa mai nagarta da addu’ar  samun tsira da rahma.

‘Yan uwa mu fadaka mu kyautata halaye da mu’amalar mu da kowa, ka da mu cuci junan mu a fili ko a boye, mu sani barin duniya tilas ne, wuya da dadi basa hana ka tafiya idan wa’adi ya cika.

Kamar yadda babu wadda yasan abinda zai faru gobe, hakanan babu ran da ta san garin da zata mutu bamu san sanadin ba ko time din tafiya..

Don haka mu dage da yin tanadi wajen yin aiyukan da’a da nisantar cutar wani, mu kiyaye kada muna raba ladan mu ga mutane ta hanyar aibata su.

Allah yasa mu ji mu bi, Allah ya jikan mu ya gafarta mana Laifukan mu da kura-kuren mu  ya kar6a mana aiyukan mu na da’a gareshi, Amin.

 

LEAVE A REPLY