Daga Anas Saminu Ja’en
Ranar 22 ga watan Maris ta kowace shekara ita ce ranar Ruwa ta duniya, kamar yadda majalissar dinkin duniya ta ayyana. A dan nazarin da na yi kashi da dama na al’ummar nahiyar Afrika ba su da wata hanyar samun tsaftataccan ruwan sha, fa ce ruwan da yake kwance a Gulbi sannan irin wannan ruwan ba shi da tsafta, wasu lokutan ma mafiya yawan al’umma basa iya samun ruwan da za su sha mai tsafta.
Akwai damuwa sosai ga me da ingancin ruwan da yake kwanciya a kasa, akan samu mutane biyu a cikin Takwas na al’ummar nahiyar Afruka ba sa samun ruwan da za su sha, a cewar wata kididdiga, wasu daga cikin su kanyi tafiya mai nisan zango wanda ya kai kilomita 4 zuwa 5 ko fiye da haka a kowace rana domin neman ruwan sha, shekarar da ta gabata hukumar lafiya ta duniya ta ce a kowace shekara ana samun kimanin mutane miliyan 3 da dubu dari 4 da ke rasa rayukan su sakamakon rashin tsaftataccan ruwan sha, wanda ya zama hanyar da tafi kowace kawo cututtuka da mace-mace a fadin duniya.
Kuma har ilah yau, dumbin al’ummar fadin duniyar nan suna shafe tsawon kowane yini domin neman ruwan amfanin yau da kullum.  Wannan yanayi ne mafi muni da al’ummar nahiyar Afrika suke bukatar taimako. Shin ko akwai mafita kuwa? Akwai mafita mai sauki da za ta ceto rayuwar mutane 6,825 a kowace rana, kuma zamu iya taimakawa ta hanyar samar da Famfuna, Rijiyoyi da kuma Rijiyoyin Burtsatse wadanda za su taimakawa mutane da dama a nahiyar Afrika samun ruwa, ta wannan hanyace mutane da dama a nahiyar Afrika za su samu ruwan sha; da raguwar adadin mutanan dake mutuwa.
Shin ta ya ya kuke ganin rayuwa za ta kasance idan babu ruwa mai tsafta?
Shi ta ya ya kuke ganin duniya za ta kasance, idan al’umma masu hali da iko suna tallafawa mutane domin samun ruwa mai tsafta saboda mutane su rayu?
Kasancewar yau ita ce Ranar Ruwa ta duniya. Wanne hali al’umma ke ciki game da samun ruwan sha a sassan daban daban a fadin Najeriya?
A karshe ina kira ga shugabanni masu rike da madafun iko da suka karbi amanar al’umma birni da kauyuka, kan cewar yakamata su waiwayi matsalar ruwa a wasu yankuna musamman kaukunan karkara wanda har yanzu akwai wuraran da ruwan Gulbi suke sha dana amfanin yau da kullum kuma ba shi da tsafta, Allah ya kyauta.

LEAVE A REPLY