Daga Rabiu Nura Rabiu
Ranar daya ga watan disambar kowacce shekara, rana ce da hukumar laifya ta duniya ta ware domin masu cutar ƙanjamau.
ME AKE NUFI DA KANJAMAU?
Kafin nayi bayani zan fara bayyana menene garkuwar jiki? Garkuwar jiki dai shi ne abinda yake kare jikin dan Adam daga dukkan wasu cututuuka dazarar wani abu da zai cutar da jiki sai ya yake shi ya kore shi ta hanyar baiwa jiki garkuwa, to ita wannan cuta ita take karya garkuwar nan sai ya zama, mutum yana cikin hadarin kamuwa da kowace irin cuta tunda cututtuka nayawo sosai a cikin iska.
Abinda ake kira aturance ”white blood cells” wanda sune bari mafi muhimmanci a garkuwar dan adam, su wadannan cuta ta kan kai hari ta lalalata su, ta rusa su sai ya zama garkuwar jiki tayi raunin da har ta mutu.
Wasu kadan daga cikin hanyoyin da ake samun cutar kanjamu sun hada da, ta jini kamar yin amfani da abin yanke farce na wanda yake dauke da cutar, ko kuma yin jima’i/saduwa da wanda yake/take dauke da cutar, yin amfani da allura wa mutum biyu ga wanda daya daga ciki yana dauke da cutar shima hanya ce ta kamuwa da cutar,ko kuma Uwa tana iya shafawa danta ko wajan haihuwa ko wajen shayarwa amma ita ba’a dauka ta wajen sumbatar mutum ko kuma shan ruwa kofi daya da mutumin da yake da ita.
Alamomin cutar sun hada da:
1. Zazzafan zazzabi
2. Mura
3. Ciwon jiki da kuma gabbai
4. Kumburin wasu sassa na jiki
5. Bushewar fata
Yawanci ana gane wadannan abubuwan sati biyu bayan mutum ya kamu da wannan cutar, a wannan lokacin mutum zai dinga yawan jin kasala da mutuwar jiki da kuma gajiya, sannan za a ga mutum yana ramewa, sannan kuma,  yana yawan gumi/zufa ko da kuwa cikin dare ne.
Ana iya gano wannan cuta ta hanyar gwaji a asibitoci da kuma wuraren gwaje gwaje da aka ware domin masu dauke da wannan cuta, sannan ana fara shan magani ne nan take daga zarar an tabbatarwa da mutum cewar yana dauke da cutar, kiyaye shan magani bisa ka’idar da aka baiwa mutum yana taimaka masa matuka.
Hanyoyin magance wannan cutar su ake kira da “antiretroviral therapy”a turance kuma ya hada da magunguna iri iri da za a bawa mutum a asibit bayan angano yana da cutar, ana samun sauki jiki in angano cutar da wuri sannan kuma an dauki matakan da suka dace na shan magani da kuma bin ka idojin likita yadda ya tsara.
HANYOYIN MAGANCE CUTAR SUN HADA DA
1.Yin amfani da kwaroron roba yayin jima’i
2.A guji matan banza
3.Yin gwajin asibiti kafin yin aure
4. A guji shan giya da magunguna na wanda suke haramtattu.
5. Kaucewa amfani da abubuwan wani kamar su burushi da raza.

LEAVE A REPLY