Sheikh Aliyu Said Gamawa
Daga Aliyu Said Gamawa
Alhamdu lillah rayuwar Baban mu mai Martaba Sarkin Katagum Alhaji (Dr) Muhammad Kabir Umar ta gudana cikin son al’ummar sa, yayi kokari wajen tabbatar da zaman mu lafiya, ya karfafa mu kan neman ilimin addini da rayuwa, ya rayu cikin yi mana addu’ar mu samu rayuwa cikin aminci. Dandazon masoya daga cikin da wajen jihar Bauchi yayin jana’izar sa ta kara fassara mana irin jagorancin da yayi mana.
Mai martaba dan Umaru ya sha faman jinya shekaru da yawa amma duk tsawon da yake kwance Sarkin mu yana nan cikin zukatan al’ummar sa don sun san burinsa na cigaban kasar sa. Allah yasa wannan jinya ta zama kaffara a gareshi, Amin.
‘Yan uwa masoyan katagumawa ku taimake mu da addu’ar Allah ya bamu jagora nagari bayan sa. Allah ya bamu mai tsoron Allah, Mai dattaku da halin son al’umma da cifaban kasar mu irin sa.
Tabbas muna cikin yanayi na jimamin wannan babban rashi, haka nan muna cikin zulumi da tunani iri-iri na wa zai gaji Baban mu… amma a matsayin mu na musulmai ina fatan mu natsu mu zauna cikin sanin cewa sai wanda Allah ya za6a ne zai gaji Sarki.
Mu sani guddirawa Allah ba ya kuskure, kuma duk abinda Allah yaso akan komi shike faruwa, mu bayi namu sai addu’a, mu zauna cikin shirin kar6ar qaddara.
Guddirawa mu sani Wallahi duk masu za6en sarki, da 6angaren gwamnati masu zartaswa za suyi komi ne cikin nufin Allah. Yanzu abin yi shine mu dage sosai wajen taya su addu’ar Allah ya datar su akan abinda yafi alheri garemu.
Mu daina yada jita-jita, mu daina nuna qagara, muyi zaman makoki cikin addu’ar Allah ya lullu6e sarki da rahama, Allah ya kyauta bayan sa, Allah ya maye mana  gurbin sa da mafi alheri a addinin mu da rayuwar mu, Amin.

LEAVE A REPLY