Comr Sunusi Mai Lafiya

Tayin da Shugaban PDP na rikon kwarya ya yiwa tsohon Shugaba Obasanjo ya gamu da cikas, tunda har shi da kansa yake furta cewar tayin da aka yi masa, bazai ta’ba dawowa Jam’iyyar PDP ba, amatsayin memba kuma ko uban Jam’iyya.
.
Ni aganina Baba Obasanjo yana fadin haka ne kawai saboda ya raina ‘yan kasar nan gaba daya, ya raina yan siyasar kasar wadan da yake gani a matsayin yaransa suke, wadan da ba su da wani ubangida a siyasance kamarsa, wanda ya zame musu abin tinkaho da alfahari, wanda hakan shi ya sanya har PDP tayi ‘barin baki wajen kara gayyatarsa, duk da cewa tun a za’ben 2015 ya kwarewa PDPn baya, bayan daya gargadi tsohon shugaba kasa mai ‘yar Malafa cikin wasikarsa me sa’darori da dama.

Har kawo yanzu kasar nan ba za ta manta da mutum kamar Obasanjo ba, wanda ya kassara kasar, ya lalata tsarin dimokradiyyar kasar, madadin ya raini dimokradiyyar data dawo a bayansa, saiya zamo silar durqushewarta da kuma yaga rigar ‘yancinta, yazamo silar daurewar cin-hanci da rashawa, badakalar halliburton na daga babban misalan wawushe dukiyar al’ummar kasa, rashin tsaro, fadace-fadacen kabilanci da Addinanci, mutumin da yaci mutuncin dokokin kasa, ya zamo silar rugujewar tsarin samar da tabbatuwar kasa dunkulalliya.

PDP na ganin har Obasanjo wani mutumin kirki ne, abin kunya ne jam’iyyar dake neman ta tayar da koma’darta tafake tana raragefen mutane irin su Obasanjo, sai dai ace muku Allah ya kara da wannan amsa da gwankin ya baku, duk da cewa shima Obasanjon borin kunya kawai ya ke yi, domin yanzu yasan mutuncinsa da kimarsa sun riga sun gama zubewa a kasa warwas, ko da yake naga babban aminin shugaba BUHARI ne.

LEAVE A REPLY