Wasu almajirai mata kan hanya

NAZARI: Yadda mabarata ke zubar da kimar Arewa

A wannan lokacin da dan Adam yakai makura wajen wayewa da sanin ciwon kai da sanin ya kamata, bai kamata ace tunanin wasu har yanzu irin na shekarun baya bane. Duniya taci gaba, al’ummomi da yawa a duniya sun samu cigaba mai dorewa kuma mai ma’ana a sha’anin rayuwa da zamantakewa, uwa uba kuma ilimi ya yawaita, ya saitawa al’umma rayuwarsu, daga duhun jahilci zuwa haske, ya bude musu duniya tarwai suka ganta, suka ga rayuwa kuma suka fahimce ta.

Ilimi shi ne gishirin zaman duniya kamar yadda masu iya Magana suke cewa. Shin meye ilimi? Wannan wata muhimmiyar tambaya ce da ya kamata ayi nazari kafin bada amsarta, wasu da dama kan dauka, sai mutum yaje makaranta irin ta zamani ya zauna a gaban malami, akan kujera malamin na tsaye a gabansa yana bashi darasi, wasu kan dauka irin wadan da suka halarci gaban irin wannan malamin sune wanda suka je makaranta, kuma sune masu ilimi, abinda aka koya musu kuma shi ne ilimi.

Ko shakka babu irin wancan tunani gurgutaccen tunani ne, domin irin wancan karatun sau da yawa nazari ne, da binciken wasu al’ummatai da suka shude. Kuma ilimi ne, da yake sunyi shi bisa tsari, shi  ne na bayansu suka dauko takardun baya suka karkade suka gyarasu tare da yi musu sabon tsari domin gudanarwa da ta dace da yanayi da kuma al’adu.

Mutanan da muka sani ko muke kira da Almajirai, galibinsu suna fitowa ne neman ilimin al’qurani, amma da yake al’adun kasar Hausa damfare suke da abubuwan da suka shafi addini, yasa aka gwama ko cakuda sha’anin karatun addini da kuma wasu larurorin rayuwa. Misali neman abincin da mutun zai ci larurar rayuwa ce, ta yadda tilas yana bukatar abinci domin yaci ya rayu, wannan it ace larurar rayuwa, ko neman suturar da mutum zai sanya ya rufe tsiraici; wannan ma lararur rayuwa ce, kuma inaga wannan ne dalilin da ya sanya hausawan dauri suka gwama wannan butaka da sha’anin neman karatun addini musamman na al’qurani.

Almajirai ko masu neman karatun al’qurani, kan mayar da kansu baya, su kaskantar da kansu da gangan ba kuma tare da bayyana hakan da zaman tawalu don neman yardar Allah ba. Almajirai kan dauki kansu ba wasu masu ilimi ba, basa nuna ko bayyana abinda suke yin na neman karatun al’qurani a matsayin wani ilimi abin alfahari. Haka ma jama’a suka tafi, idan ana batun Ilimi da nemansa, babu wasu da ke batun almajirai masu neman ilimin alqurani. Sabida yadda su almajiran da malamansu suka bayar da hoton almajiranci a idon duniya.

Wannan ta sanya ko ina musamman ma a kasar hausa ake yiwa almajiran al’qurani kallon kaskanci da wulakantarwa, balle kuma ayi batun mutanan kudu ko wadan da ba Musulmi ba. Sannu a hankali yanzu bara ta zama ba sai almajirai masu neman ilimin al’qurani ba; kamar yadda aka sani a baya, bahaushe ya mayar da kansa baya, ta yadda ko yaya mutum ya samu nakasa ko wata tawaya a jikinsa, to shi ya yadda babu abida zai iya yi a rayuwarsa, illa ya zauna mutane su bashi na annabi.

Mutune sun yadda su zama cima zaune, ba zasu iya yin komai ba, domin biyan bukatun larurar rayuwa, sun kaskantar da kansu sun zama mabarata almajirai. Irin wannan bara it ace ta janyowa mutanan Arewa kaskanci da koma baya a wajen abokan zamanmu mutanan kudu da ma na Arewa.  Don haka, tilas ne, gwamnatocin Arewa gaba dayansu su tashi tsaye haikan domin kawo karshen bara da barin yara da ake yi suna gararamba akan tituna da sunan karatun al’qurani. Kusan yanzu akan manyan tituna a jihohin Arewa da gidajen mai zaka dinga ganin dandazon Almajirai tun daga kan kananan yara da tsoffi suna bara tun daga safe har maraice, wannan abin takaici ne kuma abin kunya matuka. Ya kamata Gwamnatocin Arewa su yi tsaye, su yi aiki tukuru domin maganin wannan matsala.

Matsalar Almajiranci da bara, abu ne da jiha daya ba zata iya daukar wani mataki akai a jihar ta ba, tilas ne ayi gamammen tsari da zai hade kan jihohin Arewa baki daya. Misali a jihar kano zamanin Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, majalisar dokokin Kano tayi doka akan haramta yin bara a duk fadin jihar, har ya zama laifi ga me bayarwa da kuma almajiri me karba, amma ba’a je ko ina ba, wannan kudurin doka ya zama dan jabu, domin dai Almajirai suna nan kamar yadda suka saba suna bara kwararo kwararo a ko ina a ciki da wajen Kano. Babu kuma wani abu da ya biyo bayan hakan. Sabida haka, wannan yake nuna cewar tilas sai anyi wani tsari na baidaya ga jihohin Arewa domin kawo karshen bara da almajiranci.

Bama sukar karatun al’qurani, amma a irin wannan tsari da ake yi, malamai ko Alaramma yaje kauyuka ya kwaso yara kanana ya zo da su cikin birni suna kwana a zauruka da kofar gidajen mutane ba tare da yi musu wani tanadi na makewayi ko wajen kwana mai kyau, ko tsarin ko ta-kwana idan an samu mara lafiya ba, tilas a taka masa birki. Ana kawo yara kanana cikin birni da sunan bara ko karatun al’qurani, amma daga zarar sun bude ido sai su watsar da karatun su shiga neman kudi gadan gadan ko ta halas ko ta haram, haka ne mana, tunda almajirai kan je gidajen karuwa da gidan giya da silima suna bara suna rokon mutane.

Ana samun irin wadannan yara da ake kawowa cikin birane da sunan bara, da yawa a cikin ayyukan ta’addanci da suka hada da kwace, da sata, da zari ruga uwa uba da fashi da makami du kana samun irin wadannan almajirai a ciki. Ga shi sun lalata gari ta hanyar yin kashi a ko ina. Wannan ba zai yuwu a zauna a zuba ido rayuwar yara tana lalacewa a banza ba tare da an amfana da hazaka na irin wadannan yara da ake kawowa cikin birane ba.

Domin kuwa, shi almajiri ba shi da wani gata, babu wani mai sonshi hatta iyayan da suka haifeshi. Shi yasa sai ya tashi da kuncin kowa a ransa, yana jin haushin kowa, yana da damuwar kowa, domin babu wanda ya kula da rayuwarsa, iyayansa da ya kamata su zamar masa makarantar farko a rayuwa su rabba shi, sune suka fara yin watsi da shi, ta hanyar hannanta shi ga wani wanda ba su da wata alaka, wai shi zai kula da shi, su kuma Malaman basa yin abinda ya dace, domin da damansu idan suka debo wadannan yaran suka zube su, ba sa damuwa da wajen kwanansu, yaro ya kwana ko be kwana ba, ko yaro yaci abinci ko bai ci ba, ko yana fama da ciwo ko babu, in kaga an kula da rayuwar almajiri to sai ciwo ya galabaita shi, shima abinda za a iya yi masa kawai shi ne, a je kyamis a saya masa ja-da-yalo ko fanadol a bashi daga nan babu wani gata ko kulawa da zai samu, sai in ciwo ya ki ci yaki cinyewa sannan ne za’a tuna da iyayansa a mayar musu da shi.

Bugu da kari, yanzu irin wadannan yara da yawa raywarsu na cikin garari, domin ana samun batagari da yawa suna yin lalata da su a cikin duhun dare, da koya musu muguwar sana’a ko yin sata, ko sayar da miyagun kwayoyi. To a irin wannan mawuyacin hali da ake ciki bai kamata a zauna a zubawa rayuwar irin wadannan yara ido tana tafiya sasakai ba tare da sun amfani kansu ko sun amfanar da al’umma ba.

Dole gwamnatoci su tashi domin bullo da dabarun da za’a a hana daukar irin wadannan yara suna zuwa birane da sunan karatun al’qurani rayuwarsu tana lalacewa ba. Shirin da Gwamnatiin tarayya ta fito da shi na Noma, Alhamdulillah wani muhimmin cigaba ne, da ya sanya yanzu mutanan kauyuka, sun sake mayar da hankali akan noma sosai, musamman yanzu da mutanen birni suka bude ido da harkar ta yadda sukan je kauyuka su hayi gonaki ana yi musu noma, wannan ko shakka babu ya dan taimaka wajen raguwar kwararowar almajirai daga kauyuka zuwa birane domin yin bara ko yin wasu abubuwa na kaskanci dake zubar da kimar musulunci a idon duniya.

Bayan haka, tilas gwamnatoci su ninka kokarinsu, ta hanyar bullo da irin shirin nan da ake kira da “social security” ta yadda Gwamnati zata dinga tallafawa rayuwar wadan da suka gajiya, ko aka barsu da marayuwa kankana. Irin wannan shiri zai taimakawa rayuwar tsofaffi da mata da yara, wanda suke tagayyara sosaisakamakon rashin kulawa da suke samu sanadiyar rashin iyaye. Domin wasu mutanan akan rasu a barsu da kananan yara, ba tare da an bar musu waniabinda zasu iya yi domin daukan dawainiyarsu ba, sun zama bayin titi da ababen hawa, suna bi kwararo-kwararo suna bara wani zubin in sun samu dama har sata wasu suna yi. Su yi maka bara, in ka basu su yabeka, in ka hanasu su zageka.

Ba zai yuwu a zuba ido akan irin wannan rayuwa ana ganin ta ba tare da daukar wani mataki ba. Tsohwar Gwamnatin Shugaban kasa Goodluck Ebelee Jonathan tayi wani yunkuri mai kyau dan inganta rayuwar almajirai da makarantunsu na tsangaya, amma dai tsarin ba irinsa ya kamata ayi ba. Da ya kamata ne, makarantun almajiran a mayar das u tsarin da zai yi kafada da makarantun zamani na boko, ta yadda makarantun tsangaya suma zasu zama kamar makarantun kwana na boko, idan anyi hutu yaro ya koma gida gaban iyayansa, sannan a makaranta ana kula da batun abinci da wajen kwana da kuma lafiyarsu. Irin wannantsarin ya kamata ace anyiwa makarantun Alqurani, kuma wannan shi ne irin tsarin da zai raba almajiran da yin barace barace da sunan neman ilimin alqurani.

Sannan kuma bara irin wadda tsoffi da mata suke yi a kawo karshenta ta hanyar tsarin basu tallafi da ake kira Social Security. Hakan zai taimaka matuka wajen inganta rayuwar wadannan mutane, da kuma dawo da martabar mutanan Arewa da ta zube kasa warwas a sanadiyar bara da rook da almajiranci da muka yi shakulatun bangaro akan batunsu.

LEAVE A REPLY