TAHAJJUD
1- Yau ne daren farko na kwanaki goman karshe na watan Ramadhan, wato daren 21 ga wata.
2- Ya tabbata Annabi (saw) yana kara kokari na Ibada a cikin goman karshe na Ramadhan, kokarin da ba ya yin irinsa a wasu kwanakin.
3- Asali Allah ya shar’anta Tahajjudi a fadinsa:
{وَمِنَ اللَّيْلِ فَتَهَجَّدْ بِهِ نَافِلَةً لَكَ } [الإسراء: 79]
Tahajjudi shi ne rashin bacci da raya dare da Sallah da Ibada.
4- Annabi (saw) ya kasance yana raya dare da Ibadau a goman karshe kamar yadda ya zo a Hadisin A’isha (ra) cikin Bukhari da Muslim.
5- An shar’anta mana yin Jam’i a Sallar dare a watan Ramadhana, saboda Sahabbai sun bi Annabi (saw) Sallah a daren 23, har zuwa 1/3 na dare, da kuma daren 25, har zuwa rabin dare, da kuma daren 27, har daf da Asubah. To sai ya dena fitowa, tsoron kar a farlanta Sallar, kuma daga baya al’umma su kasa.
6- Tun daga nan sai aka dena yin Jam’in, har Annabi (saw) ya rasu, a zamanin Abubakar (ra) ma ba a yi ba, sai cikin Khalifancin Umar (ra), wata rana ya fito Masallaci cikin dare sai ya samu mutane suna Sallah daban-daban, sai ya hada su wuri daya, ya nada musu Ubayyi bn Ka’ab (ra) ya yi musu limanci. Sai Tamim Al-Dariy kuma ya yi limanci wa mata. Tun daga nan har yau al’ummar Musulmi suke yin Jam’in Sallar dare a Ramadhan.
7- Don haka mata ma ya halasta su fita Masallacin a yi Sallar daren da su.
8- Ubayyin (ra) yana yin Sallar ne raka’a 23, haka ake yi tun zamanin Umar (ra).
Wadannan bayanai duka suna cikin Muwadda Malik, Sahihul Bukhari da Muslim da “Sunanul Arba’a” da sauran littatafan Hadisi, cikin Hadisin A’isha (ra), Abu Zarr (ra), da kuma Nu’uman bn Basheer (ra) da wasunsu.
Saboda haka an shar’anta mana Tahajjudi, da yin Jam’i a cikinsa, da fitan mata zuwa Masallaci da sauran abubuwa da aka ruwato daga Salaf. Don haka wannan shi ne hakikanin Fiqhun Salaf.

LEAVE A REPLY